✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya kashe kansa ta hanyar yanke gabansa a Kano

Sai dai binciken ’yan sanda na farko-farko ya nuna cewa marigayin na da larurar tabin hankali.

Wani matashi dake zaune a unguwar Kurnar Asabe a Karamar Hukumar Dala ta jihar Kano ya kashe kansa ta hanyar yanke mazakutarsa da kwalba.

Rahotanni sun ce matashin ya jiwa kansa munanan raunuka a jikinsa, lamarin da ya kai ga rasa ransa.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma mamacin ya yi amfani da kwalba ne wajen yanke mazakutar tasa tare da yankar sassa daban-daban na jikinsa.

Kiyawa ya ce matashin ya rasu ne lokacin da ake kokarin bashi kulawa a Asibitin Kwararru na Murtala Muhammd dake Kano.

Kakakin ya kara da cewa lamarin ya faru ne ranar Lahadi, 14 ga watan Fabrairun 2021.

Ya ce, “Da misalin karfe 8:00 na safiyar ranar 14 ga watan Fabrairun 2021 da misalin, mun sami rahoto daga unguwar Musukwani dake Jakara a birnin Kano cewa wani matashi a unguwar Kurna ya kulla kansa a daki, sannan ya yi amfani da fasasshiyar kwalba wajen yanke gabansa da ma wasu sassa na jikinsa da dama.

“Da jin haka muka tashi jami’anmu wadanda suka bazama suka kuma garzaya da shi Asibitin Kwararru na Murtala Muhammd dake Kano domin samun kulawa, amma rai ya yi halinsa a can,” inji Kiyawa.

Kakakin ya kuma ce binciken farko-farko da ’yan sanda suka samu ya nuna cewa marigayin na da larurar tabin hankali wacce take tashi lokaci zuwa lokaci.