Wani matashi ya harbe mahaifinsa da danginsa su 12 har lahira a kasar Iran.
Kamfanin dillancin labaran kasar (IRNA) ya ce matashin mai shekaru 30 ya bude wa ’yan gidan nasu wuta ne saboda wata takaddama a tsakaninsu.
Babban jami’in shari’a na lardin Kerman, Ebrahim Hamidi, ya shaida wa IRNA cewa, matashin ya yi amfani “da bindiga kirar AK-47 ya harbe mutane 12, cikinsu har da mahaifinsa da dan uwansa a kusa da garin Faryab.”
Daga bisani jami’an tsaro sun harbe matashin a yayin musayar wuta a lokacin da suke kokarin kamo shi.
Bude wa taron jama’a wuta bakon abu ne a Iran, kasar da bindigar farauta kadai aka amince wa mutane su mallaka.
Amma a watan Janairu wani kurtun soja ya bude wa abokan aikinsa wuta a sansaninsu da ke yankin, inda ya kashe sojoji biyar sannan a tsere.