✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matashi ya haka daki a karkashin kasa saboda sabani da iyayensa

Wani matashi dan kasar Spain ya shafe shekara shida yana tonon rami don gina gida a bayan gidansu sakamakon sabanin da ya samu da iyayensa.…

Wani matashi dan kasar Spain ya shafe shekara shida yana tonon rami don gina gida a bayan gidansu sakamakon sabanin da ya samu da iyayensa.

Yanzu haka matashin yana alfaharin mallakar gidan da ya haka a karkashin kasa a bayan gidan.

Matashin mai suna Andres Canto mai shekara shekara 14 ya fara hakar ce a bayan gidansu da ke birnin Alicante a kasar Spain, bayan jayayyar da ya yi da iyayensa da suka hana shi shiga cikin gari sanye da kayan waka, don haka ya yanke shawarar ya zauna a gida ya fara tunanin hakar ramin.

Duk da bai shirya wa hakan ba, daga baya ya fara jin dadin hakar ramin. Andres ya ce ya rika dawowa yana kallon ramin da ya haka kuma ya ci gaba da fadada shi a kowane maraice, kuma bayan yin darasi da yamma, yakan dawo ya fadada ramin kadan-kadan.

A karshe ya gayyaci abokinsa don taimaka masa wajen ci gaba da aikin tonon ramin, kuma bayan sun hadu da abokin suna tonon ne, hakan ya sa ya zama kogo mai ban sha’awa.

“Iyayena sun so in canja tufafina don zuwa kauye, amma ina so in sa kwat din waka, don in dauki hankalin mutanen kauyen,” Andres Canto ya bayyana wa kafar labarai ta Zenger News.

Ya kara da cewa, “Iyayena sun ce, ba zan fita da sutura kamar haka ba, sai na ce: ‘Ba damuwa, zan iya nishadantar da kaina.’

Hakan ya sa na tafi bayan gidan na fara haka rami.”

Andres Canto da abokinsa suna aikin hakar ramin na kusan awa 14 a kowace rana yayin da suka kara kaimi wajen hakar. Ba da dadewa ba sai suka haka falo da daki.

Da farko, kusan komai na hakar an yi ne da hannu, inda suka yi amfanin da guga wajen fitar da kasar da suke hakowa.

An yi dakin ta hanyar kofofin shiga da wasu rubabbun marufi wadanda aka karfafa da ginshikai, da kuma yin bango na kankare don hana rugujewa.

Matashin ya yi ikirarin cewa, kayayyakin ginin da ake bukata don habaka dakin a bayan gidansu kawai sun kashe kudin da suka kai Yuro 50 (Dala 60) daidai da Naira dubu 24 da 779 da kwabo 40)

Rayuwa a cikin kogon dakin karkashin kasar yana da ’yar matsala, kamar yadda Andres ya yarda cewa, dole ne ya magance ambaliyar ruwa lokaci-lokaci idan ana ruwa, kuma kwari da dodunin kodi sukan samu hanyar shiga cikin dakin.

Duk da haka, samun dakin kansa abu ne da ya dace don kauce wa wata gazawa.

Duk da cewa, Andres ba ya rayuwa a cikin dakin karkashin kasar, a duk yini yana yawan daukar lokaci yana hutuwa a ciki.

Kuma ya tsara daki ta yadda zai iya samun siginar Intanet ta wifi zuwa wayar hannunsa da samar da wutar lantarki, har ma da tsarin na’urar dumama jiki a cikin dakin.