Wani matashi mai shekaru 27, Rabiu Suleiman, ya daɓa wa abokinsa Yunusa Muazu wuƙa, tare da yi masa mummunan rauni, a kan budurwa a yankin Gwagwalada da ke Abuja.
Lamarin ya faru ne a daren Talata a wani gidan kallon fina-finai a Unguwar Dodo.
- NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu
- Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi
Suleiman ya zargi Muazu da yin soyayya da budurwarsa wadda yake shirin Jamila Yakubu.
Faɗan ya fara ne lokacin da Suleiman ya samu Jamila da Muazu suna tattaunawa a gidan kallon fina-finan.
Suleiman, ya fusata lokacin da ya ga Jamila tare da abokinsa, sai ya tafi kai-tsaye ya hau abokinsa da duka.
A lokacin da suke faɗa , Suleiman ya fito da wuƙa sannan ya daɓa wa Muazu a gadon baya.
Wannan abu ya ja hankalin wasu daga cikin mutanen da ke cikin gidan kallon, wanda hakan ya sa aka yi gaggawar kiran ’yan sanda, kuma nan take suka tafi da Suleiman.
An kai Muazu zuwa asibiti domin kula da shi.
Kakakin rundunar ’yan sandan birnin tarayya, SP Josephine Adeh, ba ta amsa kira da saƙonnin waya kan lamarin ba.