Wasu matasan Najeriya sun gabatar da kansu domin zama mayakan sa-kai da za su taimaka wa kasar Ukraine yakar Rasha da ta far mata da yaki.
Matasan sun yi dafifi ne a Ofishin Jakandancin Ukraine da ke Abuja, inda suka rika sanya sunayensu a takardar rajistar da ofishin ya tanada.
Ana ganin mika wuyan da matasan suka yi amsa kira ne ga Shugaban Kasar Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, wanda ya bukaci al’ummar duniya da su taimaka wa kasarsa wajen yakar Rasha wadda ta kaddamar da yaki a cikin kasarsa.
Sakatare na Biyu a Ofishin Jakadancin Ukraine a Neriya, Bohdan Soltys, ya tabbatar da zuwan matasan ofisin domin a dauki sunayensu a matsayin mayakan sa-kai zuwa Ukraine.
Sai dai kuma Mista Bohdan Soltys ya shaida wa kafar yada labari ta The Guardian cewa kawo yanzu kasarsa ba ta yanke shawara game da daukar mayakan sa-kai ba tukuna.
Amsa kiran Ukraine
Idan za a iya tunawa, a sanarwa da Mista Zelenskyy ya fitar kwana uku bayan mamayar da Rasha ta kaddamar a kasarsa ranar Alhamis, ya zargi sojojin Rasha da kashe fararen hula.
A kan haka ne wasu ke ganin cewa matasan da ke mika sunayen nasu suna ganin yakin da Rasha ke yi a Ukraine zalunci ne, shi ya suke neman zuwa su sayar da ransu domin yakar cin zali.
Sai dai kuma wasu na ganin ba da zuciya daya matasan Najeriyan ke neman tarar aradu da ka domin zuwa kasar Ukraine da ke fama da yaki a halin yanzu ba.
A cewarsu, hankali ba zai dauka ba a ce dan wata kasa na kokarin zuwa wata kasa da ’yan asalin kasar da kuma ’yan Najeriya mazauna can da suka makale suke neman a dawo da su gida cikin gaggawa saboda barkewar yakin.
Wani matashi da ke zargin matasan da neman cin bulsu ya ce, “Wannan ba komai ba ne face wata dabara da matasan ke son amfani da ita su tsallaka zuwa kasashen Turai a bagas, sannan su yi layar zana.”
Wani matashi mazaunin Abuja da Aminiya ta zanta da shi ya ce, “Duk da cewa ba lallai ba ne idan ka kwashe su aka kai Ukraine din su tsira da ransu, amma na tabbata suna zuwa kasar za su fara naman yadda za su kara gaba.”
“Ba yaki za su je yi ba, kawai so suke su yi amfani da damar a kai su Turai, daga nan kuma sai a neme su a rasa.” inji shi ma wani matashin.
Ci-rani a Turai
Wannan zargin ba zai rasa nasaba ba da yadda matasa daga kasashe masu tasowa — irin Najeriya da sauran kasashen Afirka da Asiya — suke kokarin tsallakawa zuwa kasashen Turai domin samun sauyin rayuwa.
Yawancin matasan da ke zuwa Turai ci-rani daga kasashe masu tasowa suna bi ne ta barauniyar hanya ta hannun masu fasakwaurin mutane da rubabbun jiragen ruwa.
Wasu daga cikinsu kan kamu da cututtuka — ko su mutu a kan teku — ko su kare a sansanonin bakin haure, bayan wasan bera da mage tsakaninsu da jami’an tsaro a kan iyakokin kasashen da suke shiga ba bisa ka’ida ba.
A wasu lokutan kuma, wasu kan fada a hannun masu safarar bil Adama, inda suke karewa ana sayar da su a matsayin bayi, ana cire sassan jikinsu, kamar koda da sauransu, ana sayarwa masu nema da dan karen tsada.
A wasu lokuta akan tilasta wa mata daga cikinsu yin karuwanci — duk ba tare da su din sun amfana da kudaden da ake samu a kansu ba.
Duk da haka, akwai ’yan Najeriya da sauran kasashe masu tasowa da ke zuwa kasashen Turai ta halastaciyyar hanya domin neman halaliyarsu ta hanyar kasuwanci ko aikin ofis da sauransu.