Gamayyar Kungiyar Matasan Arewa sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta gudanar da bincike kan harin da aka kai kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.
Kakakin kungiyar, Malam Ibrahim Lawal ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da suka fitar a Abuja ranar Litinin, inda ya bukaci gwamnatin tarayya ta kara matakan tsaro a titunan jiragen kasar nan.
- ‘Masu jiran hukunci sun fi wadanda aka yanke wa yawa a gidajen yarin Najeriya’
- Akwai yuwuwar rabin ’yan Afghanistan su fuskanci yunwa – MDD
“Mun damu matuka da harin da aka kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, muna kira ga Gwamnatin Tarayya da rundunar sojin kasar nan da su yaki ta’addanci a fadin kasar nan.
“Yana da kyau gwamnatin ta sa matakan tsaro a wuraren ibada da makarantu da kasuwanni da bututan man fetur, saboda ’yan ta’adda na kai musu hare-hare.
“Idan ba a daina kai hare-hare ba, hakan na iya jefa ’yan kasa cikin mummunan yanayi. Duk wanda ya gaza yin aikinsa yadda ya kamata a sauke shi daga matsayinsa,” a cewarsa.
Lawal ya ayyana kudirin gamayyar kungiyar na yin hadaka da Gwamnatin Tarayya don kawo karshen matsalar tada kayar baya, garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaron da suka dabaibaye wasu sassan kasar nan.