✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasa sun yi zanga-zanga saboda tsadar rayuwa a Sakkwato

Albashi ba ya wadatar da mutane a yanzu saboda komai ya yi tsada.

Gomman matasa a Talatar da ta gabata sun yi zanga-zangar lumana a birnin Sakkwato kan matsi da tsadar rayuwa da aka tsinci kai a yanzu.

Matasa da suka kunshi maza da mata sun yi tattaki har zuwa Gidan gwamnatin jiha suna rike da kwalaye dauke da rubutu iri-iri ciki har da sakon “yunwa za ta kashe mu” da “ya isa hakan” da “muna bukatar abinci” da sauransu.

Wata mata mai suna Safiya Sa’idu da ke cikin masu zanga-zangar ta ce ba su fito domin cin zarafin kowa ba sai dai suna bukatar a gaggauta daukatr mataki domin rage matsin da ake fama da shi.

“Kwanon Shinkafa ’yar gida naira 3,800, Garin Kwaki 1500 ba za mu lamunci haka ba.

“Mutane suna mutuwa saboda yunwa inda a yanzu da wuya ka samu gidan da ake girka abinci sau uku a rana.

“Muna son aurar da yaranmu amma koma ya yi tsada a yanzu. Ya kamata gwamnati ta duba kokenmu ta yi wani abu da sauri,” a cewarta.

Shi ma wani mai suna Muhammad Kamilu ya yi kiran gwamnati da ta gaggauta samar da abinci ga mutane.

“Albashi ba ya wadatar da mutane a yanzu saboda komai ya yi tsada. Da yawan magidanta ba sa iya ciyar da iyalansu.”

Haka kuma, wani Yusuf Kabiru ya roki gwamnatin tarayya ta mayar da tallafin man fetur wanda a cewarsa shi kadai ne abin da zai samar da sauki ga talaka.