✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasa sun kone Sakatariyar Jam’iyyar SDP ta jihar Kogi

A yayin da ake shirin zaben Gwamnan jihar Kogi, wasu da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne sun kone babbar Sakatariyar jam’iyyar SDP da ke…

A yayin da ake shirin zaben Gwamnan jihar Kogi, wasu da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne sun kone babbar Sakatariyar jam’iyyar SDP da ke Lokoja babban birnin jihar a safiyar yau Litinin.

Matasan sun fara kaiwa sakatariyar harin ne tun ranar Lahadi, inda suka fara lalata wasu bangarorin ginin Sakatariyarda kuma fastocin ‘yan takara.

Shugaban jam’iyyar SDP na jihar Mouktar Atima, ya zargi ‘yan bangar siyasar jam’iyyar APC da kona masu sakatariya.