✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matasa sun fasa allon da Buhari ya kaddamar da aiki a Katsina

Matasan dai na nuna takaici ne kan matsalar tsaro da ta canjin kudi

A daidai lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yake tsaka da kaddamar da ayyuka a Jihar Katsina, wasu fusatattun matasa sun fasa allon da shugaban ya kaddamar da aiki.

Matasan dai wadanda da alama na nuna fushinsu ne da halin matsalar tsaro da ta canjin kudin da ake fama da ita a Jihar sun fasa allon bude gadar kasa Kofar Kaura da ke cikin Katsina.

Shugaba Buhari dai ya fara ziyarar aiki a Jihar ce wacce ita ce mahaifarsa a ranar Alhamis, inda ake sa ran zai bude wasu muhimman ayyuka da gwamnatin Jihar ra aiwatar.

Matasan da suka fasa allon a Katsina
Matasan da suka fasa allon a Katsina

Daga cikin ayyukan dai akwai gadar kasa ta Kofar Kaura da wajen tara ruwa da ofishin tattara kudaden shiga da hukumar kula da yanayi da babbar asibitin cikin gari na Katsina.

Kazalika, Buhari zai kuma kaddamar da kamfanin casar shinkafa wadda hamshakin dan kasuwar nan. Alhaji Dahiru Mangal, ya gina.