✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasa sun bankawa coci wuta saboda bacewar yaro a Akure

Wasu matasa da suka fusata sun bankawa cocin Sotitobire wuta a garin Akure babban birnin jihar Ondo bayan wani zargi da suka yi cewa, an…

Wasu matasa da suka fusata sun bankawa cocin Sotitobire wuta a garin Akure babban birnin jihar Ondo bayan wani zargi da suka yi cewa, an gano gawar yaro mai shekara daya da ya bace a cocin.

A watan Nuwamban da ya gabata ne yaron mai suna Gold Kolawole, ya bace a cocin bayan da mahaifiyarsa ta neme shi ta rasa bayan sun kammala shirin addu’ar da ta halarta a lokacin da ta bar yaron a sashin yara na mujami’ar, tun a wannan lokacin mahaifiyar yaron Modupe Kolawole ke zargin an yi mata bita da kulle ne aka sace yaron.

Ya zuwa yanzu dai mai cocin Alfa Babatunde yana hanun jami’an tsaron farin kaya na DSS Sai dai a zantawar da matar limamin cocin Bisola Alfa, tayi da wata kafar yada labarai a yau Alhamis ta musanta labaran da ke cewa an gano gawar yaron a cikin cocin nasu.

Matar ta koka da halin da tace mijin nata ya sami kansa a hannun hukumar DSS tun bayan faruwar lamarin.

Limamin cocin da matarsa