✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasa masu damfara a Facebook sun shiga hannu

Dubun wadansu matasa biyu, Ekong Achibong da Ndefereke Asukuo da ake zargin sun kware wajen yaudarar ’yan mata ta shafin sada zumunta na Facebook ta…

Dubun wadansu matasa biyu, Ekong Achibong da Ndefereke Asukuo da ake zargin sun kware wajen yaudarar ’yan mata ta shafin sada zumunta na Facebook ta cika a Kalaba Jihar Kuros Riba a makon jiya.
Bayanan da Aminiya ta samu sun ce matasan biyu masu matsakaicin shekaru, sun sanya hotunan ’yan mata ne a shafinsu suka rika kulla zumunta ta hanyar neman kawaye da ’yan mata kuma kowace budurwa ta ga hoton ’yar uwarta mace sai ta amince. A hankali har sai suka rika gayyato kawayen nasu zuwa gidansu. Majiyarmu ta ce idan yarinya ta zo layin ta buga waya sai su ba mace ’yar korensu wayar ta amsa kiran. Ita kuma daga nan sai ta je ta shigo da bakuwar tasu, sannan ta yi batan-dabo daga gidan, sai bayan sun gama fasikanci da ’yan matan su ce musu sai sun ba su kudi. Majiyar ta ce, yayin da suke aikata wannan danyen aiki, wani na daukar hoton bidiyonsu. Da haka ne suke yi wa ’yan matan barazana suna karbar kudi a hannun duk wadda ba ta so asirinta ya tonu.
Yadda asirin matasan ya tonu kuwa, kamar yadda aka yi wa wannan jarida bayani shi ne, matasan da suke zaune ne a wani gida a Layin Atekong a birnin Kalaba; sun gayyato wata kawarsu ce  wadda bayan ta shiga gidan sai ta iske wadansu katti biyar. Sai ta ce tana neman kawarta, yanzu suka yi magana da ita ta waya, sai suka far mata  suka yi mata fyade suka bukaci ta ba su Naira dubu 30 ko su sanya hoton da suka dauka na badalar da suka yi da ita a shafin sadarwar intanet. Bayan ta ba su kudin ne sai ta sanar da ’yan sanda, su kuma suka kama matasan biyu.
Mai magana da yawun ’yan sandan jihar,  Irene Ugbo, ta tabbatar da aukuwar lamarin kuma ta ce wata mai hulda da shafin sadarwar intanet mai suna Esame Nkim ce ta sanar da su ayyukan wadanda ake zargin. Irene Ugbo, ta ce wadanda ake zargin suna hannunsu, yayin da ake neman sauran abokan laifinsu ruwa a jallo.