✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasa 6 da ake zargi da lalata karamin yaro sun shiga hannu

Yan sanda a Jihar Jigawa sun kama wadansu matasa shida bisa zargin yin luwadi da wani karamin yaro dan shekara 13 a kauyen Harbor Sabuwa…

Yan sanda a Jihar Jigawa sun kama wadansu matasa shida bisa zargin yin luwadi da wani karamin yaro dan shekara 13 a kauyen Harbor Sabuwa da ke Karamar Hukumar Jahun.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, SP Audu Jinjiri ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ’yan sandan a Jahun sun kama mutum shida din ne sakamakon korafi da wani mai suna Abubakar Yusuf mazaunin Harbor Sabuwa mai kimanin shekara 25 ya kai musu.

Ana zarginsu ne da yin lalata da wani yaro (an sakaya sunansa) lamarin da ya sa ’yan sanda suka kai dauki kangon da suke ciki, inda  aka kama su gaba daya.

Daga cikin wadanda ake zargin akwai Mustapha Muhammed dan shekara 25 da Muhammad Datti dan shekara 30 da Adamu Ali dan shekara 25 da Gambo Idris dan shekara 25 da Muhammad Suleiman dan shekara 30 da Jibrin Salisu dan shekara 30 kuma dukkansu mazauna kauyen Harbor Sabuwa.

Kakakin ’Yan sandan ya kara da cewa sun kama mutanen  ne bayan sun yi lalata da yaron, kuma an garzaya da yaron Asibitin Jahun domin duba lafiyarsa

Ya ce su kuma wadanda ake zargin an tura su Sashen Binciken Manyan Laifuffuka na Rundunar ’domin gudanar da bincike a kansu kuma da zarar sun kammala za a kai su kotu domin a yi musu hukuncin da ya dace da su kamar yadda doka ta tanada.

Ya ja kunnen masu aikata irin wadannan halaye su canja halayensu muddin suna son zaman lafiya domin ’yan sanda ba za su yi musu sassauci ba, inda ya tabbatar da cewa duk wanda suka kama zai dandani kudarsa.