‘Yan Sanda a kasar Indiya sun ce sun fara bincike kan wasu mutum 42 da suka mutu, wasu 100 na kwance a asibiti, bayan kwankwadar gurbatacciyar giya a ranar Alhamis.
Rahotanni dai na nuna mutane 12 ne suka fara kwanciya rashin lafiya sakamakon shan barasar da ake zargin na dauke da sinadarin Methanol mai cutar da jikin dan Adam, da wani lokaci wasu kan yi amfani da shi domin hana abu daskarewa.
- Rikicin Ukraine: Shugabanni Afirka Munafikai ne –Macron
- Kisan Hanifa: Kotu za ta yanke wa Abdulmalik hukunci
Shugaban rundunar ‘yan Sandan kasar, Ashok Yadav ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP cewa mutane 31 sun rasu a lardin Botad, yayin da wasu 11 suka mutu a kusa da lardin Ahmedabad da ke kasar.
“Bincikenmu ya kai mu ga gano barasar da mutanen suka sha na dauke da wannan sinadari na Methanol wanda ya yi sanadiyar mutuwarsu,” inji Ministan Harkokin Cikin Gidan Kasar, Harsh Sanghavi a wata sanarwa da ya fitar.
Sanghavi ya ce yanzu haka an kwantar da wasu mutum 97 domin ba su magani, da kuma mutum biyu da ke halin rai kwakwai-mutu kwakwai.”
Garin na Gujarat dai, wanda nan ne mahaifar Firaministan kasar, Narendara Modi, na daga cikin jihohin Indiya da dama da suka haramta siyarwa da shan barasa.
Shugaban ‘Yan Sandan Gujarat, Ashish Bhatia ya ce mahukunta dai sun bankado wuraren siyar da barasar da dama a garin, tare da kama mutanen da ke sha da siyarwa a wurin.