✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matasa 3 sun shiga hannu bisa laifin lalata da wata yarinya

Dubunsu ta cika bayan matasan gar sun sanar da jami'an abin da ke faruwa

’Yan sanda a Jihar Bayelsa sun kama wasu matasa uku da laifin yunkurin kisa tare da yin lalata da wata yarinya mai shekara 13, sannan suka datse mata yatsa don yin tsafi.

Lamarin dai ya faru ne a Karamar Hukumar Sagbama ta jihar a ranar Litinin.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya ce an samu nasarar cafke wadanda ake zargin ne ta hanyar hadin gwiwa da matasan yankin.

Ya ce wadanda ake zargin sun kashe wasu mutum uku a yankin, duk da nufin yin tsafi da wasu sassa na jikinsu.

“Bincike ya nuna cewa wadanda ake zargin su uku dukkansu na da shekara 15 a duniya, kuma ’yan asalin yankin Sagbama ne.

“Sun kama wata matashiya mai shekara 13 suka yi lalata da ita sannan suka yanke mata yatsa.

“Bayan wasu matasa a yankin sun zarge  su ne aka sanar da jami’an tsaro kuma aka yi nasarar cafke su.

“An ceto matashiyar, sannan an garzaya da ita asibiti domin kula da lafiyarta.

“An mika wadanda ake zargin zuwa sashen binciken manyan laifuka domin gudanar da bincike mai zurfi,” inji shi.