✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matar tsohon Gwamnan Anambra ta tsinka wa matar Ojukwu mari a wajen rantsuwa

Matar tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Misis Ebelechukwu Obiano, ta tsinka wa matar tsohon Shugaban ’yan tawayen Biyafara, Bianca Ojukwu mari ana tsaka da bikin rantsar…

Matar tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Misis Ebelechukwu Obiano, ta tsinka wa matar tsohon Shugaban ’yan tawayen Biyafara, Bianca Ojukwu mari ana tsaka da bikin rantsar da Charles Soludo a matsayin sabon Gwamnan Jihar.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa lamarin ya faru ne jim kadan bayan Farfesa Soludo ya kammala rantsuwar kama aiki.

A cewar NAN, manyan baki ciki har da maidakinta, Willie Obiano na zazzaune lokacin da ta tashi ta tafi layin da Misis Bianca take zaune, sannan ta dalla mata marin.

Lamarin dai ya jawo hayaniya a wajen, kafin daga bisani jami’an tsaro su samu su yakiceta daga jikin matar Ojukwun.

Daga nan ne aka dauke ta daga wajen, inda shi ma mijin nata ya fice tun da dama an kammala rantsar da sabon Gwamnan.

An dai rantsar da Farfesa Soludo, wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ne, a matsayin sabon Gwamna bayan ya lashe zaben da aka gudanar a watan Nuwamban 2021 karkashin jam’iyyar APGA.
(NAN)