Wata kotun majistare da ke zamanta a Igbosere a jihar Legas ta aike da wata mata da ake zargi da kashe diyarta zuwa asibiti a yi mata gwajin tabin hankali.
Ana zargin matar mai suna Olufunmilola Adisa da dulmuya diyarta mai watanni 21 da haihuwa a ruwa cike da bokiti har sai da ta mutu.
Da take yanke hukunci, mai shari’a Dora Ojo ta umarci a kai Oluwanifemi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Legas don yi mata gwajin tabin hankali.
Kotun ta bayar da umurnin ne bisa bukatar hakan da Ofishin a da Kariyar Shari’a na Gwamnati Jihar Legas ya gabatar.
- An kashe mutum 70 a Sabon Birni bayan ziyarar Gwamna Tambuwal
- Wanda ya sace jikan Sheik Dahiru Bauchi ya shiga hannu
- Bude makarantu: Muna duba yiwuwar karkasa azuzuwa — Gwamnati
A ranar 11 ga watan Mayu ne ‘yan sanda suka kama Misis Adisa bayan an zarge ta da dilmiya diyarta a ruwan da ya yi ajalin diyar a gidanta da ke kan rukunin gidaje na Gowon Estate a jihar.
Daraktan ofishin kariyar shari’an Dr Babajide Martins ya ce za su tabbatar da ganin wadda ake zargin ta sami adalci, kamar yadda kudurin ofishin nasun ya tanada na samar da tallafin shari’a ga marasa galihu.
Martins ya ce za kuma su yi kokarin ganin an dauke ta daga Sashen Binciken Manyan Laifuka na jihar zuwa Asibitin Kwakwalwa da ke Oshodi har zuwa sadda za a gurfanar da ita a gaban kuliya a ranar 26 ga watan Yuni.
Daraktan ya ce yayin da ake dakon sakamakon gwajin kwakwalwar nata ofishin zai yi tabbatar ganin wadda ake zargin ta samu cikakkiyar kariya.
Ya ce hakan ya yi daidai da kudurin gwamnan jihar na ganin cewa duk wani dan jihar ya sami tallafin da yake bukata na shari’a komai talaucinsa.