✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar da ake shelar mutuwarta ta musanta hakan

Wata baiwar Allah mai suna Fadimatu Amadu Aminu ta musanta labarin mutuwarta da aka baza ta kafar sada zumunta ta Facebook a ranar Lahadin makon…

Wata baiwar Allah mai suna Fadimatu Amadu Aminu ta musanta labarin mutuwarta da aka baza ta kafar sada zumunta ta Facebook a ranar Lahadin makon jiya, inda aka sanya wani hoto da aka gani, aka rubuta sunan Fadimatu, aka yada shi ta kafar, cewa ta rasu. Kuma an sanya lambar waya inda aka nemi iyaye ko ’yan uwanta ko wani wanda ya san ta ya kirawo domin neman karin bayani.

Wani abu kuma da ya faru shi ne, idan an kira lambar babu wanda yake amsawa, lamarin da ya jefa iyaye da ’yan uwan Fadimatu a cikin damuwa, wadda Fatakwal, Jihar Ribas; inda aka shaida mata cewa ana nemanta.

Bayan ’yan uwa sun gama alhinin rashin ’yar uwarsu, sai mahaifiyar Fadimatu da wata yayarta da wani dan jagora suka niki gari daga Kalaba, suka tafi Fatakwal domin tabbatar da ko ’yarsu ce. Ita kuma Fadimatu ko waya ba ta da ita bare a ji motsinta ko labarin halin da take ciki sai aka yi sa’a da zuwansu wani wanda ya san unguwar da take ya yi musu jagora. Suna zuwa kuwa ta yi arba da yarta, inda suka rungume juna suna kuka.

Aminiya ta zanta da Fadimatu Ahmad Aminu  ta wayar mahaifiyarta, kan me za ta sanar wa ’yan uwa da abokan arziki game da jita-jitar mutuwarta da aka baza a kafar sada zumunta, sai ta ce: “Ba ni ba ce, kamanni ne suka zo daya, domin ni ma na ga hoton an nuna mini. Da na zo gida na gane cewa ba ni ba ce, kamanni ne kadai, domin tana da wani abu a fuskarta da ba ni da shi. Ina sanar da ’yan uwa da abokan arziki cewa ba ni ba ce, kamanni ne kawai. Ga ni a gida wurin iyayena.”

Wani mai hulda da kafafen sadarwa da ya nemi a sakaya sunansa, ya yi tsokaci game da lamarin, yana cewa: “A Najeiya lamarin yadda wadansu mutane ke rika fakewa da kafafen sada zumunta suna cin zarafin wadansu ya kai magaryar tukewa, domin haka tun da wuri ina kira ga gwamnati ta dauki mataki; ta kafa doka kamar yadda aka yi a wasu kasashen duniya.”