✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar ajali

Wani mutum ne ya auri wata bazawara, ranar tarewa ya shiga dakinta da dare sai ya iske ta tana ta kuka, ga huluna uku a…

Wani mutum ne ya auri wata bazawara, ranar tarewa ya shiga dakinta da dare sai ya iske ta tana ta kuka, ga huluna uku a gabanta. Ya tambaye ta: “Ko lafiya kike ta kuka haka, maimakon murna?” Shi ne ita kuma ta amsa masa da cewa: “Wannan hular ta farko, ta mijina ce na fari, kwananmu uku da aure ya mutu. Hula ta biyu, ita ma mijina na biyu ke da ita, ya mutu ne kwanaki uku da daura aurenmu. Hula ta uku, mijina na uku ne ke da ita, kwananmu biyu da aure ya mutu. Shi ya sa nake kuka, tunanin cewa ga shi na yi sabon auren mutum na hudu ko…” Kafin ma ta ida batun, sai ya aje hularsa gabanta ya ce mata: “Ga hulata nan, in za ki ba da labari, sai ki ce ta mijinki ce na hudu, wanda ya gudu a ranar farko da daura aure!”
Daga Aminu Marbels Bazza Sakkwato 08060903721