Zababben Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP, ya yi alkawarin cewar matansa da ’ya’yansa ba za su samu wani mukamin da zai ba su damar shiga sharafin gwamnatinsa ba.
Yusuf, wanda ya bayyana hakan jim kadan bayan karbar takardar shaidar lashe zaben Gwamna a ofishin INEC da ke jihar, ya bayyana hakan ne kan yadda ake zargin iyalan gwamna Abdullahi Umar Ganduje suka yi tasiri wajen tafiyar da gwamnatin jihar.
- HOTUNA: Yadda INEC ta bai wa Abba shaidar lashe zaben Gwamnan Kano
- Zazzabin Lassa ya kashe mutum 142 a Jihohi 23
Zababben gwamnan ya ce ba zai bai wa iyalansa damar shiga gwamnatinsa ba saboda ba tare aka rantsar da su ba domin yi ea al’ummar Jihar Kano aiki ba.
“Matana ba za su kasance a cikin gwamnati ba. ’Ya’yana ba za su kasance a cikin gwamnati ba. Kuma ina tabbatar muku da cewa Mataimakina ma hakan ce za ta kasance,” a cewarsa.
Abba ya bukaci dan takarar Gwamna na jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna da sauran wadanda suka yi takara da su zo a yi tafiya tare don ciyar da Jihar Kano gaba.
“Mun samu labarin Gawuna ya sanar da kafafen watsa labarai kafin bayyana sakamakon zabe cewa idan bai yi nasara ba, zai karbi abin da Allah Ya kaddara. Don haka muna kira a gare shi da ya fito ya ja hankalin mutanensa su yarda da cewar wannan yin Allah ne,” in ji shi.
Ya ja hankalinsu da su yi koyi da jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya fadi zabe a 2003 amma ya taya wanda ya lashe murna.
Da yake magana game da gudunmawar jami’an tsaro a lokacin zaben Gwamna a Jihar, Abba ya gargadi jami’an tsaron da suka hada kai da jam’iyya mai mulki da su guji aikata hakan a gaba, inda ya bukace su da su fifita hidimta wa ‘yan Najeriya ba tare da nuna wariya game da jam’iyya, addini ko kuma kabilanci ba.