Wani binciken jin ra’ayin jama’a da Aminiya ta gudanar ya gano cewa da yawa daga cikin ’yan mata a wannan zamani sun fi son kudi fiye da komai daga bangaren maza a zamantakewar soyayya.
Binciken dai ya gudana ne a dandalin sada zumunta na Facebook, inda mutane suka bayyana ra’ayoyinsu a kan dalilan da za su sa mace ta so namiji.
- Rikicin Kazakhstan ya ci rayuka fiye da 220 —Gwamnati
- An yi Sallar Jana’izar mutum 15 da gobarar New York ta kashe
Binciken ya bi diddigi ra’ayoyin jama’a kan dalilan da ke iya sa mace ta so namiji, inda yawancin mutanen da suka yi tsokaci a kai sun bayyana cewa tabbas yanzu mata a wannan zamani idan ka ga sun so namiji to yana da abin hannunsa.
Ya kara da cewa “Dukiya mana. Ko akwai wani abu a zamanin nan da yake burge mata a gun namiji sama da wannan?”
“Bayan kasancewa mutum yana da kudi, har ila yau, ya kasance bai damu da abin hannun nasa ba, ma’ana zai iya bayarwa a kowane lokaci aka bukata.”
Sai dai wasu na ganin ba wai iya kudi ne dalilin da ya ke sa mata su so namiji ba, wasu abubuwa kamar tsafta, nutsuwa, hankali kan sa mace ta so namiji kamar yadda Muhammad Muhammad ya bayyana.