✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matan da suka fi tashe a Najeriya a 2020

Mata 10 da ba za a manta da su ba a shekarar 2020 a Najeriya

Yayin da ake ban kwana da shekarar 2020, Aminiya ta yi waiwaye kan wasu mata da labaransu suka yi tambari tare da daukar hankali a Najeirya a cikin shekarar.

Labaran wadananan mata guda 10 sun yi tashe a shekarar ce saboda jarumta, fice, ce-ce-ku-ce da sauransu daga fannonin rayuwa daban-daban na rayuwa. Ku biyo mu:

1. Tolulope Arotile

Marigayiyi Tolulope Arotile

Labarin mace ta farko mai tuka jirgin saman yaki a Najeriya, Flight Officer Tolulope Arotile ya yi tashe a 2020 bayan da ta kai hare-hare da jirgi a kan maboyan ’yan bindiga a yankin Arewa ta Tsakiya.

Hafsar Sojin Sama, mai shekaru 20 na cikin aikin yaki da ’yan bindigar ne labarin rasuywarta ya karade Najeriya.

Kasar ta kadu da rasuwar Tolulope wadda ta samu yabo a matsayin jaruma mai kishin kasa kuma abin koyi ga matasa musamman mata.

Tolulope ta gamu da ajalinta ne a Barikin Sojin Sama da ke Kaduna, sakamakon hatsarin mota.

2. Rahama Sadau

Jarumar masan’antar Kannywood Rahama Sadau ta karade shafukan sada zamunta bayan da wani ya yi tsokacin batanci ga Manzon Allah (SAW) a kan hoton da ta wallafa a shafinta na Twitter.

Batancin ya jawo caccaka da la’anata har sai da jarumar ta fito a wani bidiyo ta bayar da hakuri tare da wanke kanta da cewa ba za ta taba yarda ta yi abin da zai kai ga batanci ga Manzon Allah (SAW) ba.

Rahama Sadau a lokacin da take ba da hakuri ga al’ummar Musulmi.

Bayan wani bawan Allah ya aike wa ’yan sanda takardar korafi kan lamarin batancin, an yi ta baza jita-jitar cewa ’yan sanda sun tsare ta kuma kotu ta daure ta.

Rahama Sadau ita ce mace daga yankin Arewacin Najeriya da aka fi neman bayanai a kanta a Google a 2020, abin wasu ke gani yana da nasaba da ce-ce-ku-cen da ya shafe ta.

3. Aisha Yesufu

Daya daga cikin jagororin BringBackOurGirls masu neman dawo da ’yan matan Chibok ta kara yin tashe a 2020 musamman lokacin zanga-znagar #EndSARS.

Labarinta ya karade shafukan zumunta musmman bayan ganin ta sanye da zumbulelen hijabi a cikin masu zanga-zangar ta neman rushe sashen ’yan sandan SARS da ake zargi da cin zalin jama’a musamman matasa.

Yayin da wasu suka yabe ta  da cewa ta yi abin kai, wasu kuma sun yi ta caccakar ta da cewa ana amfani da ita ne domin rusa Arewa.

Lamarin ya kai sai da ta sanya a shafinta na Twitter cewa ana yi mata muguwar addu’a a masallatai saboda zanga-zangar.

Aisha Yesufu a lokacin

Aisha Yesufu ta kuma yi kaurin suna wurin sauke wa gwamnati lodi ta hanyar caccaka.

A karshe-karshen 2020, ta yi ta musayar yawu a Twitter da Mashawarcin Shugaba Kasa kan Shafukan Zumunta, Bashir Ahmed, game da gazawar Gwamnati.

4. Aisha Buhari

Matar Shugaban Kasar Najeriya, Aisha Buhari na gaba-gaba cikin wadadan suka karade shafukan zumunta a shekarar.

Jami’an tsaronta sun bude wuta a cikin Fadar Shugaban Kasa bayan cacar baki tsakaninta da hadimi kuma dan uwan Shugaba Buhari, Sabi’u wanda aka fi sani da Tunde.

Jijiyoyin wuya sun tsahi ne a lokacin da ta yi takakkiya zuwa gidanshi a Fadar Shugaban Kasa don ta sa shi ya killace kansa bayan dowarsa da Legas, inda a lokacin cutar coronavirus take ganiyarta.

Shi kuma ya ce sam, Shugaban Kasa ya sahale masa, lamarin ya da kai ga cacar baki a tsakaninsu.

Da cacar bakin ta yi zafi ne masu tsaronta suka fara harbi (abin da ba a taba ji ba a Fadar) shi kuma ya ketara katanga ya arce.

Shugaban ’Yan Sandan Najeriya ya janye masu tsaron nata, matakin da ita kuma ta yi ta kalubalantar sa a kai.

Hajiya Aisha Buhari

Aisha Buhari ta kuma yi tashe a shekarar bayan da ta wallafa wani sako da maudu’in #Acecijama’a da kuma #ArewaMuFarka.

Ana ganin sakon nata wanda ya yi tashe, hannunka mai sanda ne kan matsalar tsaro da ta addabi yankin Arewa ga gwamantin mijinta.

5. Maryam Booth

Bidiyon tsiraicin da aka fitar na jarumar Kannywood Maryam Booth ya ja ce-ce-ku-ce a kafafe daban-daban.

Maryam Booth ta zargi tsohon saurayinta, Deezel da fitar da bidiyon da ta ce an dauka ne shekaru da dama da suka wuce domin aibata ta.

Sai dai Deezel ya musanta zargin fitar da bidiyon mai tsawon dakika uku, kuma kara da cewa babu abin da yin hakan zai kare shi da shi.

Booth ta kuma yi tashe a shekarar bayan da ta lashe kyautar kyautar Jaruma Mace Mafi Iya Mara Baya a Kayutar Fina-finan Afirka (AMAA) na shekarar 2020.

Maryam Booth

Maryam Booth ta samu kyautar ce saboda rawar da ta taka a fim din ‘The Milkmaid’.

Ta doke wadda ta zo a matsayi na biyu, Chairmaine Majeri, wadda ta taka makamanciyar rawar a fim din ‘Mirage’sai kuma Linda Ejiofor a fim din ‘4th Republic’ a matsayi na uku.

 

5. Sadiya Umar-Farouk

Labarin kanzon kurege na auren Ministar Agaji Sadiya Umar Farouk da Babban Hafsan Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Air Marshal Sadique Abubkar na daga cikin wadanda suka yi tashi.

Rade-radin aurenta da Sadique shi ne na biyu bayan makamancinsa da aka yi ta yadawa a bara cewa Shugaban Kasa Buhari ya angwance da ita.

Tuni dai Air Marshal Sadique ya karyata da ake yi ta bazawa cewa an yi auren ne cikin sirri a wani masallaci da ke unguwar Maitama a Abuja.

Ministar Agaji da Jinkai Hajiya Sadiya Umar Faruk
Ministar Agaji da Jinkai Hajiya Sadiya Umar Faruk

7. Fatima Ridabu

Labarin Fatima, diyar Nuhu Ribadu, tsohon Shugaban Hukumar  EFCC mai yaki da almundahada ya karade gari inda aka zarge ta da bayyana tsiraici a lokacin bikin aurenta.

Surutan da ta sha a shafukan zumunta bayan fitar hoton auren da ta sanya dogouwar riga fara mai shara-shara daga samanta ya kai ga sai da ta nemi afuwar jama’a.

“Kamarar rigar mai ruwan kasa da na sanya ce aka gani kamar fatata ce – ba zan taba yin haka ba,” inji Fatima Ribadu.

Fatima da minjinta (mairawani) tare da surukinta da wasu mahalarta daurin auren

Ta ci gaba da cewa, “Duk da haka na dauki laifin kunyatar da hakan ya jawo wa ’yan uwana da abokan arziki, na kuma dauki darasi.”

Sai dai amaryar ta Aliyu, dan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakatar ta yi takaicin yaduwar hotunanta da ta ce a cikin gida suka dauka amma aka baza su a shafukan zumunta.

8. Maryam Sanda

Hukuncin kisa ta hanyar rataya da kotu ta yanke wa matar da ake zargi da kashe kashe mijinta, ya dauki hankali matuka.

Ra’ayoyi sun bambanta kan wadda aka yanke wa hukuncin wadda a lokacin take dauke da jaririyarta, diyar mijinta Bilyaminu da ake zargin ta kashe shi.

Maryam wadda ta fashe da kuka tare da sallallami bayan alkali ya karanta hukuncin ta dauka kara, amma Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin.

Yanzu ana jiran shari’ar da ta daukaka zuwa Kotun Koli ne a kan hukuncin da kotunan suka yanke mata.

Maryam Sanda rike da diyarta, bayan fitowa daga kotu

9. Ngozi Okonjo-Iweala

Tsohuwar Ministarla Kudi da Tattalin Arziki, Ngozi Okonjo-Iweala ta zama babban labari a Najeriya da ma duniya bayan da ta shiga takarar Shugaban Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO).

Okonjo Iweala wadda ake gani saura kiris ta kai ga gaci ta samu goyon baya a cikin gida da kasashen duniya, inda Shugaba Buhari ya ce Najeriya na goyon bayanta kai da fata.

Wasu labarai sun yi ta cewa ta kai bantenta amma daga baya hukumar WTO ta ce da saura tukuna.

Tsohuwar Ministar Kudi da Tattalin Arzikin Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala

10. Hanan Buhari

Amfani da Jirgin Shugaban Kasa da Hanan, diyar Shugaba Buhari ta yi zuwa wani taro a Jihar Bauchi ya tayar da kura inda ’yan Najeriya suka yi ta tofa albarkcin bakinsu.

Daga baya dai Fadar Shugaban Kasa ta fito ta bayyana cewa ’ya’yan Shugaba Buhari na da damar yin amfani da jiragen Shugaban Kasa.

Bikin daurin auren Hanan ya yi tashe sosai a Najeriya inda wasu matasa biyu masoyanta kuma ‘yan a-mutunta suka bayyana.

Da kyar da jibin goshi aka samu aka shawo kan na farkon wanda ya yi yunkurin kashe kansa saboda ta yi aure, ya rasa ta.

Na biyun kuma ya ce ya rumgumi kaddara tunda bai samu cikar burinsa na auren ta ba, amma ya yi alkawarin shanu hamsin domin a yi shagalin bikinta.

Sai dai kowanne daga cikin matasan biyu babu wanda ya taba yin ido hudu da diyar Shugaban Kasar, wadda ta shafin zumunta kawai suka san ta.

Hasali ma ba budurwar kodaya daga cikinsu ba ce.