Wasu daga cikin matan da aka sace daga yankunan kananan hukumomin Rafi da Shiroro na jihar Neja a bara sun kubuta daga hannun masu garkuwa da su da ciki, wasu kuma da jarirai.
Ana dai zargin cikin da ’ya’yan na ’yan ta’addan da suka yi garkuwa da su ne kuma suka rike su tsawon shekara guda kafin ’yan sanda su kubutar da su a makon da ya gabata.
An dai shaida cewa hudu daga cikin matan na cikin mutum 25 din da aka sace a garin Allawa da ke kan hanyar Pandogari zuwa Allawa, lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa daga cin kasuwa a watan Fabrairun baran.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ’yan ta’addan ne dai suka dauki hayar motar bas domin ta dauki mutum 24 daga kauyen Palu-Waya na karamar hukumar Shiroro da ke jihar, domin canza musu wuri.
Yayin da wasu majiyoyi, ciki har da na ’yan sanda ke cewa ana kokarin kai matan ne jihar Kebbi, wasu kuwa sun ce dajin Kainji ake Shirin kai su, kamar yadda suke zargin ’yan ta’addan sun umarci direban motar.
Sai dai lokacin da suka kai Kagara da ke karamar hukumar Rafi, sai daya daga cikin matan ta bukaci direban ya tsaya za ta yi fitsari.
Bayan tsayawar tasu ne ta kwalla ihun neman taimakon da ya kai ga kubutar da su tare da kama direban, wanda yanzu haka yake hannun ’yan sanda.
Wata majiya daga cikin ’yan sanda ta tabbatar wa Aminiya cewa yanzu haka matan na tsare a hedkwatar ’yan sandan jihar Neja da ke Minna, babban birnin jihar.
Majiyar ta kuma ce an sami kunshin albarusai a cikin jakar daya daga cikin matan.
Kazalika, ya ce daya daga cikin wadanda suka kubutan na cikin ’yan matan makarantar Sakandaren Chibok da ke jihar Borno da aka sace tun a shekarar 2014.
Majiyoyi daga garin na Allawa sun shaida wa wakilinmu cewa an kubutar da matan ne a cike da motocin bas guda biyu a ranar Lahadin da ta gabata, lokacin da ’yan ta’addan da ke zargin ’yan Boko Haram ne ke kokarin canza musu wuri daga dajin na Allawa.
Sai dai mazauna yankin sun ce dole sai an kai matan wajen gyaran tunani saboda dadewar da suka yi a hannun ’yan ta’addan, inda suka ce wasu daga cikinsu na cewa sun fi so su ci gaba da zama da ’yan ta’addan har zuwa karshen rayuwarsu.