Salam Edita, don Allah ka ba ni dama na yi tsokaci dangane da matakin da sabon Shugaban kasar Najeriya Muhammad Buhari dangane da yunkurin daya fara dauka na magance matsalar tsaro musamman yadda shugaban ya fara da ziyarar kasashen Afirka musamman makwabtanmu. Hakika hakan yana nuna mana shugaban da gaske yake yi zai yi maganin rashin tsaron da ke damunmu saboda rashin tsaro shi ne babban kalubalen da ke damunmu don haka mu talakawa ‘yan Najeriya muke goyan bayan wannan tsarin tare da addu’ar Allah Ya taimaki wannan yunkurin.
Daga Aminu Abdu Sani mai Nagge, Kano, 08099479880.
Kira ga Shugaba Muhammadu Buhari
Yakamata Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya duba mutane masu kishin kasa wajen nada su ministoci.
Daga Lawal Muhammad Hayin Ojo Zariya.
Yaba wa Aminiya
Salam Edita, muna yaba wa aikinku. Jaridar Aminiya it ace jagorar dukkan jaridun harshen Hausa a wannan karni. Saboda ita ba ta Ingausa, ba ta maimaita abin da ta buga, ita ma yakamata ta yaba wa kanta kamar yadda wasu suke yabon kansu, amma ba ta yi. Muna son a dawo mana da hira da tsofaffin ’yan jarida da hira da rayayyun mutanen da Mamman Shata ya yi wa waka. A kowane mako idan ban sami jaridar Aminiya ba, ba na jin dadi. Allah Ya kara daukaka.
Dags Sani Dala, 08036800241.
Kira ga Gwamnatin Jihar Jigawa
Salam. Ina kira ga sabuwar Gwamnatin jihar Jigawa don Allah mai girma Gwamna Alhaji Muhammad Badaru ina ba ka shawara. Idan za ka taimaka wa kananan hukumoni, mu mutanen Jahun idan z aka yi hakan ka bi ta hanyar mutanen ka wato na kusa da kai. Domin idan ka bi ta hannun ’yan Jahun za su bata maka aiki. Mu kuma bah aka muke so ba. Mu gyara muke so da ci gaban jiharmu da kauyukanmu. Allah Ya taya ka riko.Amin summa amin.
Daga Muhammad Mini Jahun, Jigawa.
Taya Gwamnan Jigawa murna
Salam Edita, don Allah ka ba ni daman a taya Gwamnan Jihar Jigawa wato Muhammad Badaru Abubakar da Mataimakinsa Barista Ibrahim Hassan Hadejia fatan alheri. Allah Ya taya su riko.
Daga Yunusa Hamza Hadejia, 07030303616
Fatan alheri ga Gwamnan Jihar Bauchi
Assalamu alaikum Editan Aminiya, ka ba ni dama in mika sakon fatan alheri ga sabon Gwamnan Jihar Bauchi Barr M.A Abubakar da kuma mataimakinsa Injiniya Nuhu Gidado da fatan an shiga ofis lafiya.
Allah ya basu sa’a da nasara wurin ciyar da Jihar Bauchi gaba muna kira ga gwamnatin jihar wanda talakawa suka zaba da hannunsu da ta bincika gwamnatin da ta gabata musamman ma kudin kananan hukumomi wanda gwamnatin baya wanda Isa Yuguda ya jagoranta tayi warwaso da su. Hakazalika, ina kira ga gwamna Abubakar da ya yi mana zaben kananan hukumomi ya kawo karshen mulkin kama karya wanda ya saka kananan hukumomin cikin mummanan yanayi. A karshe ina bai wa gwamna shawara akan da ya mai da hankalinsa akan noma da kiwo musamman ma saya wa manoma kayan aiki wato tractoci da kayan aikin sarrafa amfanin gona domin yau a Jihar Bauchi ba mu da tracta na noma wanda sukakai guda 10 wanda gwamnati ta saya domin inganta harkan noma da noman rani da tona dam-dam da kiwon kifi da kaji a hurar da matasa domin a gaskiya gwamnatin baya tayi watsi da aikin gona. Muna fata gwamnatin za ta kawo dauki a harkan noma a jihar.
Daga Ahmadu Manager Bauchi, 08065189242
Kan binciken wasu jami’an Babban Bankin Najeriya
Hakika badakalar da aka binciko wasu jami’in Babban Bankin Najeriya (CBN) nayi, abin Allah wadai ne, ya kamata hukumar EFCC su kara zage damtse da zakulo masu ciki da fadi da dukiyar kasa suna almundahana da ita.
Daga Hafizu Balarabe Gusau, 07035304499
Taya sabbin shugabanni murna
Salam Editan Aminiya. Ka ba ni dama don na taya zababbun Shugabanninmu wadanda aka rantsar murna, kamar su: Shugaban kasa Muhammadu Buhari, da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad el-Rufai da sauran gwamoni duka. Allah Ya ba su ikon cika alkawuran da suka daukawa talakawansu.
Daga Mudassir Ibrahim Mando Jihar Kaduna, 08024122559
Fatan alheri
Aminiya ku ba ni dama na taya Shugaba Muhammadu Buhari murna. Allah Ubangiji Ya ba shi ikon yin adalci.
Daga Aminu Yusuf