✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matakan Rubuta kagaggun Littattafan Hausa

Rubutu rayayyen al’amari ne da kan wanzu matukar wanzuwar duniya, kuma tamkar shuka ce wacce in har ka yi za ta girma ta ba ka…

Rubutu rayayyen al’amari ne da kan wanzu matukar wanzuwar duniya, kuma tamkar shuka ce wacce in har ka yi za ta girma ta ba ka inuwa ka kuma ci ‘ya’yanta. Yana kuma iya zama tamkar dan kunama ko kuma kaikayi wanda Hausawa ke cewa “koma kan mashekiya”.
Bisa abin da masana rubutu ko labarai suke cewa, kagaggen rubutu shi ne, duk wani labari da aka kirkira a aka rubuta shi, gajere ko dogo don ilimtarwa ko  nishadantarwa ko yada wata manufa ko kuma don a tayar da zaune tsaye, akan yi shi a suffar zube ko wasan kwaikwaiyo.
Tarihin kagaggun littattafai bai dade ba sosai a kasar Hausa idan aka kwatanta da tarihin samuwar wakokin baka da kuma rubutattu. Wakoki sun samu kulawa tun shigowar Musulunci kasar Hausa, da yake an yi amfani da su wajen yada addinin Musulunci.
Su kuwa kagaggun littattafai ko kuma rubuce-rubuce sai bayan da Turawa suka shigo kasashenmu na Afrika ta Yamma ne suka fara samuwa. Yawancin rubuce-rubucen da Turawa suka yi ba na kagaggun littattafai ba ne.
Littafin da Schon J.F. ya rubuta mai suna “Farawa Letafen Magana Hausa”, shi ne littafin Hausa na farko na zube cikin boko. Duk rubuce-rubucen da Turawan suka yi babu wanda ya yi kama da kagaggun labarai wato Nobel, sai dai a bugun karshe a shekarar 1886, ya tabo tatsuniyoyi. Kuma yawancin littattafan na yada addinin Kiristanci ne.
Amma rubuce-rubucen zube na ‘yan kasa ya samo asali ne sakamakon kafa hukumar talifi ta Arewa (Northern Literature) a shekarar 1933, inda ta sa gasar rubuce-rubuce ga ‘yan kasa, inda suka samar da littattafai guda shida kamar haka: Ruwan Bagaja na Abubakar Imam, 1935 da Gandoki na Bello Kagara 1935 da Jiki Magayi na Tafida Umar da Dr. R.M. East, 1935 da Idon Matambayi na Muhammadu Gwarzo 1935 da Shehu Umar na Abubakar Tafawa balewa 1935 sannan da Iliya danmaikarfi na Ahmadu Ingawa 1968.
Zuwa yanzu kuwa ana da littattafan kagaggun labarai sama da dubu hudu, wadanda marubuta maza da mata suka rubuta.
Idan aka ce matakan rubuta kagaggun littattafai ana nufin hanyoyi ko dabaru ko wasu tubala ko kuma wasu abubuwa da ake so mai rubuta kagaggun littattafai ya tanada ko ya yi amfani da su a duk lokacin da ya tashi rubuta ire-iren wadannan kagaggun littattafai, don haka a wannan bangare za mu duba ire-iren matakai ko hanyoyi ko tubala da ake amfani da su wajen rubutun.
Abu na farko da mai son rubuta kagaggen littafi na Hausa zai fara tanada shi ne tunani. Tunani shi ne babban abu a wajen mai rubuta kagaggen littafi don in babu tunani ko kuma in ba a yi tunanin mai ake so a rubuta ba babu rubutun littafin gaba daya.
Mai son rubuta kagaggen littafi zai tanadi abin da yake so ya rubuta wato labari, shin labarin soyayya ne ko na jarumta ko na yara ko na aljanu ko kuma wani daban. Don yin hakan shi ne zai sa ya san alkiblar da ya dosa, kuma ya sami saukin isar da sakonsa, in bai tanadi labari ba akwai matsala don ko ya zauna don rubutun abin ba zai yiwu ba.
Shi kuma labarin ba sai mutum ya san komai da komai na cikinsa ba, amma dai zai fi kyau in an san daga inda aka tashi da kuma in da za a sauka. Amma sauran abubuwan da ke cikin tsakiyar labarin sai ka zo rubutun sannan za ka same su, a lokacin da basirar rubutun take saukowa.
Yana da kyau mai rubuta kagaggen littafi ya yi wa littafinsa suna kafin ya fara ko kuma kafin ya gama, domin sanya wa littafin suna yana taimaka wa mai rubutun labarinsa ya dinga tafiya da sunan littafin. Wasu lokutan ana samun littafi da aka gama rubutawa ba a sanya masa suna ba, sai daga baya a zo ana ta kame-kamen yadda za a sanya masa suna, wanda da an ba shi suna tun farko da ba a sami wannan matsala ba, kuma labarin zai fi tafiya da sunan sosai.
Ya kamata mai rubuta littafi ya lura da lokaci da kuma wurin da yake rubutun, abin da ake nufi a lura wajen sanya lokaci, kamar kwanakin wata ko shekaru don kada a dinga samun rikicewar lissafin shekarun ko watanni, don ana iya samun rikicewarsu in ba a kula ba. Haka ma batun wuri, idan kana rubuta littafi mai bayar da labarin rayuwar birni ko karkara, ka tabbata abin da kake rubutawa a cikin labarin karkara yana faruwa a karkarar, haka abin da kake rubutawa na game da birni ka tabbata suna wakana.
Yana da kyau a duk lokacin da mai rubutu ya zo yin rubutu a kan wani abu da aka san yana bukatar bincike, to a bincika shi don kada a rubuta shi da ka yadda zai zo ya rudar da mutane musamman ma wadanda ba su san shi ba. Misali abin da ya shafi lafiya da shari’a da al’adu da kuma addini.
Duk wanda yake rubuta kagaggun littattafai na Hausa yana da kya ya kula da addininsa da al’adunsa a lokacin rubutunsa, tun da an ce adabi madubin al’umma ne, idan ka rubuta wani abu da ba na al’adarka ko addininka ba, mutanen da ba su san wadannan abubuwa ba za su dauka haka kake a fannin al’adarka da addininka. Kuma zai zama kana tallata al’adun wasu ne a matsayin naka.
Akwai wasu sunadarai ko tubala wadanda idan aka hada su yayin rubutu kagaggun littattafai musamman na soyayya sun fi dadi da armashi, kamar: Sunayen mutanen da suka dace (Taurari) da Siffanta mata masu kyan hali da kyawun halitta da ayyana ire-iren mataye ko mazajen da mafi yawan mutane suka fi so, da bayyana kyawawan halaye na iyaye da ’ya’yansu da sauransu.
Sunadaran sun hada da niyayya da Fito da abubuwan da namiji ya fi son mace ta yi masa, da Fito da abubuwan da mace ta fi son namiji ya yi mata, da Fito da abubuwan da ke faruwa a rayuwa ta zahiri dangane da soyayya, musamman a rayuwar ma’aurata, sannan yanayin soyayya bayan ta rikide ta zama aure, da kuma amfani da kalmomin soyayya masu dadi da faranta zuciya, Da sauransu.