Babu shakka dole ne kowane mutum ya zama yana da mutanen da ya amincewa da su a rayuwa. Kamar yadda ango yake da abokai haka ma matar take da kawaye, wadanda ta amince da su, amma wani lokaci irin wadannan kawaye ne ke cin amanar ma’auratan har ta kai sun kashe musu aure.
Wasu daga cikin kawayen amarya da abokan ango sun san abin da suke yi, kuma soyayyar da suke nuna wa ango da amarya ta Allah da Annabi ce, amma wasu babu abin da suka kudurce a zuciyarsu sai bakin-ciki da tsurku da tsugudidi. Wasu ma kawayen daga bisani amarya take gamuwa da su bayan ta tare a gidanta, inda masu kananan shekaru da ’yan mata masu zuwa hira da kallon fina-finai da matan aure makwabta da masu sayar da kayayyaki iri-iri da kuma dattijai da tsofaffi masu zuwa hira tare da yin gulmace-gulmace.
Idan aka yi rashin sa’a aka samu amarya ba mai nisan tunani ba ce, sai irin wadannan kawaye su fara kawo mata maganganu iri-iri. Har wani lokaci su rika gaya mata cewa ai sun ga mijinta da wance ko kuma sun gan shi a wuri kaza. Ita kuma daga nan sai ta hau kan abin da aka fada mata ba tare da ta yi bincike ba, ta rika fushi tana zare idanu tana cika tana batsewa. Shi kuwa angon ya rasa laifin da ya yi mata. Ta haka shi ma idan ba mai nisan tunani ba ne sai ya yi zuciya, shi ma ya rika yin fushi, ya rika daure mata fuska. Daga nan sai alaka ta lalace a fara kai kashedi wurin iyaye da waliyyan da suka daura auren.
Idan kuwa aka yi sa’a amaryar ko angon masu zurfin tunani ne za ka ga irin wadannan miyagun kawaye ba za su ci nasara a kan su ba, saboda sun san duk gutsuri-tsomar da suka kawo musu ba za su yarda da ita ba, balantana ma su amince da gulmace-gulmacen da ake yadawa a tsakaninsu.
Amaren da suke da kulaficin kawaye, wadanda duk wacce suka gani sai su yi kawance da ita su jawo ta jika ba tare da tantancewa ba, su ne suka fi fadawa cikin wannan tarko don ba kasafai namiji ya fiye yin abota mai zurfi ba kamar mace. Su mata suna da saurin yarda da amince wa juna. Irin amaren da suke tara kawaye a gidajensu babu shakka suna cikin hadarin fadawa tarkon gulma da yamadidi, kuma idan ba su yi hattara ba alakarsu da mazajensu na cikin hadari.
Akwai wacce da ta tara kawayenta sai ka ji ta saki baki ta kwashe duk abin da ya gudana tsakaninta da mijinta ta fada musu, su kuma su yi ta dariya. Wasu da suke jin haushin ta a cikinsu sai su kuma su kwashe su gaya wa mijin ko ’yan uwansa, daga nan sai a fara rikici. Wasu kawayen kuwa sai su yi amfani da abin da suka ji daga amaryar su yi kulle-kullen da za su yi su hada alaka da mijinta su ja hankalinsa ta dabara su yi ta yi mata sharri har ya sake ta su kuma su aure shi.
Wasu kawayen ma irin matan nan ne da suka kashe auransu sai su dawo su tare a gidajen amare su yi ta kulle-kulle har sai sun ga sun kashe wa duk amaryar da suka hadu da ita aure. Za ka ji suna yi wa amaren karyar cewa auren dole aka yi musu ba kaunar mazan da suka aura suke yi ba, ko ka ji suna gaya mata cewa sai ta tashi tsaye idan ba haka ba uwar mijinta da ’yan uwansa za su hana ta jin dadin aure. Kuma su ce mata sai ta tashi tsaye ta nemi maganin da za ta mallake mijinta. Daga nan sai su sanya ta a hanyar bin bokaye da ’yan bori.
Abubakar ya rubuto ne daga Jihar Legas. 08027406827