Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Ga karashen mukalar da muka fara kawo muku a makon da ya gabata.
Babban abin takaici shi ne mafi yawan samari da suke irin wannan soyayya suna yi ba don aure ba, suna yi ne don wata bukata . Da zarar sun gama cin moriyar ganga sai kuma su yada korenta, idan muna maganar soyayya to ya kamata mu sani cewa ba lallai ba ne sai irin wadda muke gani a cikin fina-fanai musamman na Indiya da kuma irin soyayyar cikin littafi ba, duk irin wadannan soyayya suna wuce makadi da rawa, amma duk da haka sai ka ga da irin wannan soyayya wasu suke koyi, shi ya sa abubuwa suka cabe. Idan kuka yi wa irin wannan soyayyar kallon tsanaki za ku ga kazantar da ke cikinta ya fi alfanunta yawa.
Lokutan baya ba a san irin wannan ba. Wani lokaci ina tare da kakana muna hira yake fada mini cewa, a baya budurwa ba ta san ma mene ne zaben saurayi ba ballantana har ma ta rika fita da sunan zance, duk wanda aka ce shi ne mijinta babu yadda za ta yi da shi za ta zauna, kuma haka shi ma saurayin iyayensa suke zaba masa matar da zai aura, amma abin sha’awa a haka za ka ga auren nasu ya dade ba tare da wata matsala ba. To amma a wannan lokaci kafin irin haka ta faru sai an kai ruwa rana, ba na jin hakan za ta iya faruwa. Domin matan yanzu sun fi son a bar su su zabi mijin aure da kansu koma bayan zabin iyayensu, wanda hakan take kai su ga zaben tumun dare.
Na sha karanta labarai a jarida inda wasu matan ke kashe kansu ta hanyar shan guba ko rataye kansu, saboda an hana su auren wanda suke so. Kuma idan za mu kwatanta da irin wancan auren na baya da kuma na yanzu za mu ga cewa auren baya ya fi nagarta fiye da irin na yanzu, wanda aka dauki lokaci ana yi masa soyayya. To ashe dai ba sai an yi irin wannan soyayya ba aure yake karko ke nan? Ko a tarihin musulunci babu irin wannan soyayyar. Amma idan ka yi niyyar yin aure addini ya ba ka dama ka kalli wadda kake so daga kasa har sama musamman kirar jikinta domin ka ga abin da zai kara jan hankalinka, sannan ganin kirar jikinta ne zai tabbatar maka da lafiyarta, domin ka samu nutsuwa, wanda yake kokwanton haka ya tambayi malamai za su yi masa bayani sosai don ya kara samun gamsuwa. Sannan idan muka yi la’akari da iyaye da kakanni za mu ga cewa ba irin wannan danbarwa suka yi ba wadda muke kira da soyayya, amma a haka suke cin nasarar zamantakewar aurensu.
To ko mene ne abubuwan da ya kamata mu duba don kawo sauyi daga irin wannan muguwar al’ada? To na farko dai iyaye su ne ya kamata su san wane ne yake zuwa wajen ‘yarsu, kuma da wace manufa ya zo domin tabbatar da haka kuwa shi ne, da zarar saurayi ya zo kada ku ba shi dama har sai kun binciki halayensa, idan kun gamsu da halayensa sai ya turo magabatansa domin manya su shiga cikin magana. Daga nan iyaye za su iya ba shi dama domin ya zo su tattauna da wacce yake so din, idan ta amince sai a kafa masa sharuddan zance, misali a ba shi dama ya zo a sati sau biyu, kuma da rana ba da dare ba, sannan ya zamana wajen zancen nasu waje ne da mutane za su rika giftawa ba. Indai saurayi da kyakkyawar manufa ya zo to zai yarda da wannan sharadi.
Na biyu ya kamata ‘yan mata su rika bambanta tsakanin aya da tsakuwa, a nan ina nufin su rika bambancewa tsakanin mai son su da gaskiya da kuma mai yin soyayyar sheke aya, za su iya fahimtar hakan ta halayensa da maganganunsa. Na uku samari da ‘yan mata su guji kwaikwayon soyayyar fina-finai da ta littafi. Na hudu ya kamata samari da ‘yan su sanya tsoron Allah a zukatansu musamman maza domin matsalar tafi daga bangarensu, su sani duk abin da suka yi da ‘yar wani to su ma sai an yi da tasu. Za a samu ci gaba idan aka rage irin wannan soyayyar ta bayan fage. Allah Ya sa mu dace.
Ibrahim Ibb Kazaure
07031616267 ko 08183908615
DUNIYAR MA’AURATA
Idan maigida ya ki adalci…
Assalamu alaikum makarantanmu, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Yau kuma za mu tattauna hukuncin da shari’a ta aje in maigida ya ki wanzar da adalci tsakanin matansa, da kuma sauran bayanan da suka danganci adalci da raba daidai yayin zaman aure da mace sama da daya, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Adalci:Sai kun yi kafin a yi muku
Sharadi na farko game da wajabcin adalci da raba daidai daga maigida tsakanin matansa shi ne, su ma sai sun yi masa adalci; adalcin da za su yi masa kuwa shi ne, su ba shi dukkan hakkokinsa na aure da suka rataya a kansu, don haka a shari’ance, maigida yana iya janye wasu hidimomin rayuwar aure kamar ciyarwa ga matar da ba ta ba shi hakkinsa na ibadar aure, ko wacce ba ta yi masa ladabi in ya ce kada ta yi, sai ta yi, in kuma ya hane ta, ta ki hanuwa.
Adalci: Mata sai kun yi hakuri da kau-da-kai
Mun sha jin cewa duk dan Adam ajizi ne, tara yake bai cika goma ba, to haka ma a wajen bangaren adalci cikin rayuwar aure, komai irin dagewar maigida ga yin adalci tsakanin matansa, wata sa’in sai ajizancin nan na dan Adam ya bayyana, don haka dole sai mata sun daure sun rika kawar da kai ga ‘yan kananan abubuwa na rashin adalci daga wajen mazajensu, wadanda ba su taka kara sun karya ba, wadanda kuma ba wata muguwar cutarwa a cikinsu, in suka ce ko dan yaya suka ga wani abu sai sun tanka za su iya tayar da hankalinsu da na maigida ne kawai a kan abin da bai kai ya kawo ba. Don haka dole sai an yi hakuri kuma an kai zuciya nesa kan kananan abubuwa, sai in rashin adalci ya zama babba ko kuma karamin da ake yawan maimatawa, to a irin wannan ne dole sai mace ta nemi abi mata hakkinta.
Idan maigida ya ki adalci…
Ga macen da mijinta ya ki wanzar da daidaitaccen adalci gare ta cikin abubuwan da suka wajabta ya yi gare ta, watau kiri-kiri ya karkata sosai ga abokiyar zamanta ta yadda yana danne mata hakkokinta masu yawa da ke cikin aure, to tana da zabi uku don kwatar ‘yancinta:
1. Na farko ta sanar da waliyyinta ko wani wakilin waliyyinta, da ya same shi ya yi masa nasiha tare da hankaltar da shi irin ba daidai din da yake aikatawa, ya shawarce shi a kan tsayar da adalci kamar yadda shari’a ta aza a gare shi da ya yi.
2. Idan ya ki daukar wannan shawara da nasihohi da hankaltowa, to tana iya kai shi kotun musulunci, in alkali ya tabbatar da rashin adalcinsa, sai ya umarce shi da lallai sai ya aikatar adalci nan.
3. Idan duk da haka ya yi watsi da umarnin alkali ya ki yin adalcin, to tana da zabin ko ta nemi saki, ko ta yafe masa wanzar da adalci gare ta idan ta ji zama da shi ba adalci ya fiye mata rabuwa da shi.
Maigida ka sani…
A cikin adalci, bayyana bambanci ne ba a so, watau a bayyane, so ake ka yi hulda da matanka kan siga iri daya ta kowace fuska, kulawar da za ka ba su ta zama iri daya, amma can in ka kadaita daga kai sai daya daga cikinsu, ta yadda sauran ba su gani; to a nan maigida sai ya ci karensa babu babbaka.
Ba a so kuma a zake da yawa wajen yin adalci nan, watau kar ya zamanto saboda kwadayin son yin adalci a boye son da ake ma wacce aka fi son, ko ma ya kasance ana cutar da ita don kada ta gane ita ce mowa ko don kar sauran su gane an fi sonta, bayyana so da kauna halal ne, don haka kar maigida ya haramta wa kans abin da Allah Ya halatta masa. Dubi misalin Annabinmu fiyayyen halitta, wanda kowa ya san ya kai matuka wajen yin adalci tsakanin al’ummarsa kuma musamman tsakanin matansa RA, amma duk da haka a bayyyane yake kowa ya san ko wace ce mowa cikinsu; kuma idan an tambaye shi, kowa ya fi so cikin mutane duka, baro-baro yake fadar gaskiya ba ya yin wata kwana, don haka wacce Allah Ya sa ta zama ita ce aka fi so cikin mata, ba daidai ba ne a danne ko a boye son nan don tsoron kar a yi rashin adalci, abin da ake so dai maigida ya dage su ma sauran mata ya biya musu dukkan hakkokinsu daidai da irin wanda yake ba wacce ya fi so din, ta yadda ba ta inda za su yi kuka da shi. Domin su ma ai yana son su tun da har ya auro su, son na su ne dai bai kai nata ba, wannan kuma a cikin ikon Allah SWT yake.
Maigida: Idan ka ki yin adalci…
Annabi SAW ya ce duk magidanci da ya kasance ba ya yin adalci a tsakanin matansa, to ranar lahira za a tashe shi barin jikinsa a shanye, duk kuwa wanda aka tayar da wata mummunan kama ranar lahira, to alama ce ta cewa da wuya sakamako ya yi kyau, don ‘yan aljanna ba a tashinsu da mummunar kama. Don haka maigida, ko don kaunar kanka da ceton kan wuyanka daga wuta, sai ka dage ga yin daidaitaccen adalci tsakanin matanka; ka tuna Allah SWT, bayan ya tabbatar da cewa mazaje ba sa iya yin adalci wajen soyayya da sha’awa komai yaya suka so yin haka din, sai kuma ya ce SWT: “Kada ku karkata dukkan karkata har ya kasance kun bar dayar kamar wacce aka rataye,” mu lura da cewa ‘dukkan karkata’ na nufin komai kankantar karkata, don haka magidanta a dage kada a karkata ga wadda aka fi so, in har za ku wanzar da adalci cikin gidajenku, hakan zai haifar da tabbatuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidajenku, kuma da wuya mata su rika yawan fadace-fadace, sai dai su hada kansu su zama aminan juna.
Zan dakata a nan, sai mako na gaba in sha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a kodayaushe, amin.