✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Mataimakin Shekau’ ya mika wuya ga sojoji

Tun bayan mutuwar Shekau ake ta samun karuwar ’yan Boko Haram da suke mika wuya ga sojoji.

Bayanai sun ce wani jigon Kungiyar Jama’atu Ahl as-Sunnah Lid-Da’wati Wa’l-Jihād (JAS) da aka fi sani da Boko Haram, Alhaji Ari-Dafinoma ya mika wuya ga jami’an tsaro a Arewa maso Gabas.

Tun bayan mutuwar Shugaban Kungiyar Abubakar Shekau ne ake ta samun karuwar ’ya’yan kungiyar da suke mika wuya ga sojojin Najeriya, kamar yadda BBC ya ruwaito.

Ana ci gaba da samun bayanai a baya-bayan nan game da batun mika wuya ga sojojin Najeriya da ake cewa wannan jigo na Boko Haram ya yi.

Alhaji Ari-Dafinoma wanda shi ne Mataimakin marigayi Shugaban Kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya yanke shawarar mika wuya ne bayan da ’ya’yan Kungiyar Boko Haram da ta abokiyar hamayyarsu ta ISWAP fiye da 52,000 suka mika wuya ga sojojin Najeriya.

Wata majiya ta ce Alhaji AriDafinoma ya mika wuya ne ga sojin birged na musamman na 21 da ke Bama a Jihar Borno a ranar Lahadin da ta gabata.

Majiyar ta ce hakan ya faru ne sakamakon tilasta masa fitowa daga maboyarsa, a wani barin wuta da sojoji suka yi a inda ’ya’yan ƙungiyar suka kafa tungarsu.

Sai dai kuma wata majiyar ta shaida wa BBC cewa ’ya’yan Kungiyar Boko Haram sun kashe Alhaji Ari-Dafinoma, yayin da suka farga yana niyyar mika wuya ga sojojin.

Tun bayan mutuwar Abubakar Shekau ake ganin lagon kungiyar ya karye, kuma rudani ya kutsa a cikinta, har wadansu daga cikin ’ya’yanta da jigoginta suka shiga mika wuya ga sojojin Najeriya.

Wasu majiyoyi da dama sun yi ittifaki cewa, wani muhimmin dalili da ya tilasta wa Alhaji Ari Dafinoma yanke shawarar miƙa wuya, shi ne saboda mummunan fadan cikin gida da ake gwabzawa a tsakanin Kungiyar Boko Haram da bangaren abokiyar hamayyarta ta ISWAP.

Wannan adadi na mutum 52,000 ya kunshi mayakan kungiyar da mutanen da aka tilasta wa zama dakarun kungiyar da kuma iyalansu.