Mataimakin Gwamnan jihar Bauchi kuma Shugaban Kwamitin Yaki da Annobar Coronavirus a jihar, Sanata Baba Tela ya harbu da cutar.
Mai Taimaka wa Gwamna Bala Muhammad na Musamman kan Yada Labarai Mukhtar Gidado ya ce mataimakin gwamnan ya killace kansa bayan an tabbatar da kamuwarsa.
Sanarwar ta ce Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta yi wa Sanata Baba Tela gwaji bayan ya nuna alamun cutar ta coronavirus.
“Ya harbu da cutar ne yayin sauken nauyin da ya rataya a kansa na jagorantar yakar annobar COVID-19 a jihar Bauchi,” inji sanarwar.
- Ba mu janye dokar kulle kwata-kwata ba – Gwamnatin Kano
- Dan majalisar jihar Kano ya sha da kyar
- Galibin kananan hukumomin da suka fi masu COVID-19 a Legas suke
Yanzu haka “NCDC ta dauki jinin dukkan wadanda suka yi mu’amala da shi domin tantance matasyinsu.”
NCDC ta kuma umurce wadanda suka yi mu’amala da mataimakin gwamnan su ci gaba da killace kansu har sai sakamakon gwajinsu ya fito.
Gwamna Bala Muhammad wanda shi ne farkon wanda ya kamu da cutar a jihar Bacuhi amma ya warke ya bukaci jama’a su sa mataimakin nasa a addu’a.