Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa FRSC, ta tabbatar da mutuwar mutum 17 a sakamakon wani mummunan hatsari da ya auku daren ranar Asabar a Karamar Hukumar Akwanga ta Jihar Nasarawa.
Kwamandan sashin rundunar na Akwanga, Ebere Onyegbaduo ne ya tabbatar da faruwar lamarin da cewa, “mun samu kiran neman agaji da misali karfe 7 na dare a sakamakon wani mummunan hatsari da ya auku a garin Agwada da ke tsakanin garin Akwanga da Gudi.”
- Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 50 a Zamfara
- An saki iyalan Kansila bayan biyan fansar Naira miliyan 4
- ‘Yan ta’adda sun harbe wani mutum a Kano
“Mun yi gaggawar isa wurin da lamarin ya faru sai muka tarar da wata motar haya kirar Sharon da kuma wata motar gida kirar Sienne suna ci da wuta dukkaninsu dauke da mutane a cikinsu.
“Mun kira Hukumar kashe gobara inda aka samu nasarar kashe wutar da misalin karfe 11 na dare sannan muka kammala aikin ceton da misalin karfe 2 na dare.”
Mista Ebere ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa motar Sharon din ta taho daga Abuja inda yayin yunkurin ketare wasu motocin da ke gabanta ta ci karo da motar Sienna inda nan take wuta ta kama wadda ta yi sanadiyar konewar mutum 17 da ke cikin motocin biyu ta yadda ba a iya gane su.
Ya ce mutanen da ke cikin motar Sharon din an killace su a babban Asibitin Akwanga yayin da kuma na cikin motar ta Sienna aka mika su Asibitin Kwararru na Dalhatu Ashraf da ke birnin Lafia.
Mista Ebere ya gargadi direbobi a kan kiyaye dokokin tuki musamman kauracewa gudun da ya wuce ka’ida domin tseratar da rayukansu da kuma ta fasinjoji.
Daga bisani an gano cewa mutanen da ke cikin motar Sienna wani ma’aikacin Hukumar Sadarwa ta Kasa ne Yarima Nuhu Hamma da mai dakinsa da kuma ’ya’yansu.
Rahoto ya nuna cewa suna kan hanyarsu ta zuwa Abuja ne yayin da karar kwanan ta cimma su bayan sun ziyarci ’yan uwa a garin Gashaka da ke Karamar Hukumar Sardauna a Jihar Taraba.
Marigayi Nuhu Hamman Gabdo shi ne mai rike da rawani Ubandoma na masarautar Gashaka.