✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata masu ciki dubu 75 ke mutuwa cikin dubu 100 a Sakkwato

A cikin mata masu juna biyu dubu 100, dubu da 75 ke mutuwa a Jihar Sakkwato saboda karancin kayan gina jiki. Daraktar Kula da Rigakafi a…

A cikin mata masu juna biyu dubu 100, dubu da 75 ke mutuwa a Jihar Sakkwato saboda karancin kayan gina jiki.

Daraktar Kula da Rigakafi a Hukumar Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Dokta Hadiza Bodinga ta bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hukumar USAID da ACTION NIGERIA mai suna ‘Albishirinku’.

Shirin an fitar da shi ne da nufin magance mace-macen kananan yara da mata masu juna biyu.

Ta ce a cikin mutum miliyan 5.3 a Jihar Sakkwato, masu dauke da juna biyu sukan kai dubu 265 da 667.

A cewarta kashi 24.3 ke zuwa asibiti yin awon ciki sauran suna haihuwa a gidajensu saboda karancin ilimin da suke da shi.

Ta kara da cewa cikin masu zuwa awon kuma kashi 21 ne kadai ke sake zuwa asibiti bayan sun haihu a binciki lafiyarsu.

A  jawabin Uwargidan Gwamna, Hajiya Mariya Aminu Waziri Tambuwal ta ce Gwamnatin Jihar Sakwato, tana kokari don ganin cewa mata da kananan yara sun samu ingantacciyar lafiya ta hanyar samar da abubuwan da suke inganta kiwon lafiya a kowane mataki, da suka hada da samar da kwararrun ma’aikata da magunguna da samar da shirye-shiyen wayar da kan al’umma da sauransu.

“Gwamnatin Jihar Sakkwato na kokarinta na ganin cewa an rage yawan mace-macen mata masu juna biyu da kananan yara. A kan haka ne gwamnatin ke maraba da shirye-shiyen irin wannan domin ba da tallafi a bangaren, musamman na Hukumar USAID.

“Zan yi amfani da wannan dama domin gabatar da wannan shirin na ‘Albishirinku’ a Jihar Sakkwato, shirin da ya kunshi hanyoyi da dama domin wayar da kan jama’a da ilimantar da su matakan da suka dace su dauka a kan inganta lafiyar mata da kananan yara da samar da abinci mai gina jiki da kuma kariya daga zazzabin cizon sauro. Ina kira ga jama’ar Jihar Sakkwato su karbi wannan shiri da hannu bibbiyu domin alheri ne,” inji ta.

Ta kara da cewa: “Ina mika godiyata ga Kwamitin Tuntuba da Ilimantar da Al’umma kan Gyara Halaye (SBC-ACG) bisa kokarin da yake yi don ganin an samar da ingantaccen kiwon lafiya da kuma wayar da kan al’umma a kan abubuwan da suka shafi kiwon lafiya a Jihar Sakkwato.”