Misis Saraya Agidi daya ce daga cikin matan Najeriya da suka kafa kungiyar matan Najeriya (National Women Society Of Nigeria). Ta shugabanci kungiyar a kasa. A yanzu ita ce shugabar kungiyar a Jihar Nasarawa. A tattaunawarta da wakilinmu John D. Wada a Lafiya ta bayyana nasarori da kalubale da kungiyar ke fuskanta a halin yanzu inda ta kuma shawarci mata da ka da su karaya a harkar siyasa duk dab a su samu dama day a dace na shugabanci da wakilci a zaben da ya gabata ba. Ga yadda hirar ta kasance.
Tarihin rayuwata
Ni ce shugaban kungiyar matan Najeriya reshin Jihar Nasarawa. An haife ni a yankin rayawa na Jankwai da ke karamar hukumar Obi a nan jihar Nasarawa. Na yi makarantar firamare a CMS da ke garin Agyaragu inda a lokacin zan iya tunawa an koya mana sana’oi da dama. Kuma turawa ne suke zuwa su koya mana wadannan sana’oi kamar yadda a ke yin saka da dinki da sauransu. Zan iya tunawa a lokacin da kanmu muke dinka kayan makarantanmu don a na koya mana yin haka. Daganan na ci gaba da karatuna a wata makaranta da a ke kira Home Economic training centre da ke Riom a jihar Filato inda na samu takadar sheda dina a fannin tattalin gida watau Home economies. Daganan na fara sana’a kafin daga bisani na samu aiki a matsayin mai bada shawara a kan harkokin cikin gida a karamar hukumar Lafiya. Bayan nan a ka daukaka matsayi na zuwa mukaddashin darakta a fannin noma. Sai na ci gaba da karatuna a jami’ar Jos inda na samu difuloma dina a wajen. Na kuma ci gaba da karatu har ila yau a jami’ar inda na samu babbar difuloma a fannin shugabanci. Dana sake dawo gida sai na cigaba da karatu a kwalajin koyon aikin nama da ke nan Lafiya inda na samu babban difuloma di ta biyu. Da na kammala karatuna ne na shiga wannan kungiyar matan Najeriya da na bayyana maka a baya. Na shugabanci kungiyar ta kasa na wasu lokuta sannan daga baya a ka tura ni kasar Ukraine inda na wakilci matan Najeriya a wani babban taron matan na duniya baki daya. Sai daga baya a ka turoni jihar nan. Ka ga wannan kungiyarmu kamar yadda ka sani kungiya ce da a ko da yaushe ke kulawa da ci gaban matan Najeriya baki daya a duk inda suke. Muna tabbatar da cewa matan Najeriya sun samu duk wani abu da ya cancanta su samu wato a duk lokacin da za a danne musu hakinsu a matsayinmu na shugabanninsu muna tashi ne mu tabbatar ba a yi hakan ba. Muna kuma hada kai da duk gwamnati mai ci don ganin a na kulawa da mata. A halin yanzu dai kamar yadda na bayyana maka ni ce shugabar kungiyar a nan jihar Nasarawa. Ina da aure da ‘ya’ya takwas.
Halayen da na koya gun iyayena
Iyayena sun koya mani kyawawan halaye da dama. daya daga cikinsu shine yin ladabi da biyayya. Sun koya mani wannan sosai. Don sau da yawa su kan tabbatar mana cewa duk yaro da ya tashi da kyawawan ladabi, Allah zai albarkace shi. A makaranta ma na firamare abinda a ke koya mana kenan kullum. Ba shakka hakan ya taimakawa rayuwata sosai.
Na biyu kuma shine iyayena sun saba mani da aiki ta hanyar koya mani in kauda lalaci a duk harkoki na. Su kan tashe ni da wuri in yi aikin gida idan na gama kuma in je makaranta kuma har yanzu da na yi girma na saba da hakan. Na kan tashi in yi aikin gida in kuma tafi ofis da wuri wasu lokuta ma za ka ga ina jira mutane a ofis ba wai wani ya jira ni ba. Sabo da haka a gaskiya wadannan abubuwa da iyayena suka koya mani ina cin moriyarsu yanzu.
Matsaloli da kungiyarmu ke fuskanta
Muna fuskantar kalubale da dama a kungiyarmu musamman wanda ya shafi karamcin kudi. Don kamar yadda ka sani kungiyarmu tana zaman kanta ne ba ta gwamnati ba ce. Kuma ba a biyanmu kudin wata. Mu kan nemo kudi wa kungiyarmu ne da kanmu ta hanyar bayar da gudumawa a tsakaninmu mambobin kungiyar. Yanzu kowa na kukar babu kudi, wa za ka je ka ce ya taimake ka? Komai ya canza babu sauki