✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata da suka fi kamuwa da Cutar Daji

Watan Oktoba Amurka ta ware domin gangamin wayar da kan mutane a kan cutar daji. Suna kiranta Oktoba mai ruwan hoda. Kuma mutane da dama…

Watan Oktoba Amurka ta ware domin gangamin wayar da kan mutane a kan cutar daji.

Suna kiranta Oktoba mai ruwan hoda. Kuma mutane da dama a Najeriya  suna aiwatar da ayyukan domin ita wannan wata.

Wata gidauniyar cutar daji a Amurka ta ce mace daya a cikin takwas a kasar amurka za ta kamu da wannan cutar a rayuwarta. Kuma cutar dajin mama ta fi sauran cututtukan daji illa ga mata, domin mata a kasashe da dama har da Najeriya suna kamuwa da wannan cutar.

Alamomin wannan cutar sun hada da fitar ruwa jawur daga mama, kumburin wani bangare, da lotsewa ko ganin canji a yanayin girman su.

Duk da cewa wannan cutar ta na iya kama mata da maza, mata sun fi kamuwa da ita.

Mata daga shekara 45 zuwa sama sun fi zama cikin hadarin kamuwa da wannan cutar. Hakan ya sa ya kamata su rika zuwa gannin likita domin a  duba su akalla sau daya a shekara. Sannan duk wata su rika duba kansu a gida.

Matsalar da ake samu a kasar nan shi ne rashin gano wannan cuta da wuri. Ya kamata mata su sani cewa gano wannan cutar da wuri yana da muhimmanci wajen magance ta.