Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Ga karashen rubutun da muka fara kawo muku a makon da ya gabata.
Lokacin da wani abokina dan acaba yake ba ni labarin cewa ya dauki wata yarinya ‘yar makaranta ta ce masa ya kai ta ta sayi magani, shi kuma sai ya wuce da ita shagon magani suna sauka ta ce masa kai ba ka san inda za ka kaini ba? Ya ce mata shi bai sani ba. Daga nan ta ce masa su wuce gaba sannan ya kai ta wani waje inda ya ce wallahi bai taba tsammani ana sayar da irin wadannnan magunguna a wurin ba, saboda wurin ba shagon magani ba ne, amma cike yake da masu saya kuma mafi yawansu mata. Bayan sun je ne ta mika kudi aka ba ta suka dawo. Abin bakin ciki shi ne, bayan ta sauka sai take cewa “yau Allah ya hada ni da bagidajen dan acaba”.
Ka ji wata sabuwa? Wai saboda bai san inda ake sayar da kayan maye ba, don haka ya zama dan kauye. Yanzu dai abin ya yi nisa tun suna jin kunya har sun fara fitowa fili domin ko da ba su sha a gabanka ba, to kana ganinsu ka san halin da suke ciki, domin idan suna cikin wannan yanayi ba su ganin girman kowa, kuma za su rika nuna wasu dabi’u na shashanci da rashin sanin abin da ma suke fada.
Hujjarsu ita ce idan suka sha suna samun kwanciyar hankali da natsuwa, wasu kuma talauci ne yake jefa su ciki, wasu kuma tasirin kawaye ne ko kuma samarin da suke tare da su. Ko ma dai mene ne wannan ba hujja ba ce da za su fake da ita duk wanda ya lalace shi ya lalata kansa.
Lokaci ya yi da iyaye da sauran jama’a ya kamata su tashi tsaye su zage damtse domin ceto rayuwar ‘yan mata musamman a wannan lokaci da abin ke kara kaimi wajen lakume tarbiyyar ‘ya’ya mata. Me ya sa na ce mata? Dalilina shi ne kowa ya san ‘ya mace an santa da kunya da kuma da’a fiye da namiji a lokuta da yawa, kuma idan mace daya ta samu tarbiyya to kamar al’umma ne suka samu, sanin kowa ne idan aka samu mace marar tarbiyya to da wuya ‘ya’yan da suka taso a gindinta su samu cikakkiyar tarbiyya. Domin uwa ita ce take kusa da su fiye da uba, wannan ne dalilin da ya sa al’umma suka tsayu kan cewa duk mai son ‘ya’yansa su taso cikin tarbiyya to ya sama musu uwa tagari. Wannan shi ne dalilin da ya kamata jama’a tare da hukumomin da abin ya shafa su zage damtse wajen kawo karshen wannan mummunar dabi’a wadda kurarta
ke kara kadawa ko’ina a sassan kasar nan, domin duk yadda mutane suke kallon wannan bakar dabi’a tafi karfin tunaninsu nesa ba kusa ba, hausawa sun ce tsira da mutunci ya fi tsira da dukiya.
A karshe kuma ina fata wadannan ‘yan mata har da matan auren da suke shan kayan maye su gane shaye-shaye za su lahanta rayuwarsu, za su kuma lalata tunaninsu hade da daidaita rayuwarsu, wanda maimakon su yi dariya sai kuma su kare da cizon yatsa, lokacin da ba za su iya canza halin da suka samu kansu a ciki ba.