Burin kowane dan Adam ya samu kariya daga kowace irin cuta, ta yadda zai kasance cikin koshin lafiya da annashuwa da farin ciki, amma lamarin ba haka yake ga wasu matan da kuma maza ba, saboda kamun da wasu cututtuka suka yi musu.
A yau cututtuka sun dabaibaye jama’a sun saka su cikin tsaka-mai-wuya, domin babban tashin hankalin shi ne, cututtukan da dama ba sa jin magani. Wannan ne ya sa ake yi wa wasu cututtukan lakabin kabari-kusa da kanjamau da cutar sanyi da makamantansu. Kuma mata su ne suka fi shiga cikin hadarin kamuwa da wadannan cututtuka.
Wasu matan daga mazajensu suke daukar cutar, wasu kuwa daga bandaki, wasu ko aljanu ne suke sanya musu, wasu ma garin neman gira suke rasa ido, wato ta hanyar yin amfani da wasu magungunan karin ni’ima ko mayukan shafawa kamar mayukan canja launin fata da na rage kiba. Saboda da haka mata a yi hattara.
To amma cutar da ta fi addabar mata a yanzu ita ce, cutar ciwon sanyi, wacce da dama ta janyo rabuwar aure saboda zargin fasikanci da ya shiga tsakanin ma’auratan. Wasu ma ’yan mata ne da ba su taba yin aure ba, amma da sun kamu da irin wannan cuta, sai maza su rika gudunsu su ki auren su. Alamar kamuwa da cutar ciwon sanyi ta hada da jin kaikayi a al’aura, ko zubar da farin ruwa, ko kuma kuraje su rika fitowa a al’aura ko kuma ciwon mara mai tsanani . Hakazalika cutar shafar aljanu ita ma ta zama alakakai ga mata, inda wasu lokutan aure yake mutuwa saboda mazan sun kasa hakurin jure halin da matansu suke ciki. Su kuma samari sai su guji yarinya su ki aurenta saboda aljanu sun dabaibaye ta.
Wani abu da yake daure kai shi ne, yadda matan da mazan ba sa iya jure halin da suka shiga, ta yadda za su dukufa neman magani na gargajiya da na zamani da na addini, domin ganin sun samu waraka cikin rufin asiri ba tare da tonon silili ba. Halin ko-in-kula da wasu mazan da matan suke nunawa shi ma ya kara dagula lamarin, a maimakon idan ma’aurata ko saurayi da budurwa suka fahimci daya ya kamu, to su hada kai su yi magani tare, sai a rika zargin juna da tonon silili har sai dangi sun ji abin da yake tsakani.
Abin da mutane ba su gane ba shi ne, akwai cututtukan da ake daukar su ta wasu hanyoyin da ba na jima’i ba, kamar cutar ciwon sanyi akan iya daukar ta a bandaki, ita ma cutar kanjamau likitoci sun yi ittifakin cewa a kan iya kamuwa da ita ta wasu hanyoyi na daban, kamar karin jini da sauransu. Mafita shi ne, ma’aurata su daina zargin juna da fasinkanci, su tashi tsaye wajen ganin sun samu waraka daga cutar da take damun su.
Wani ma shi ne yake sanyawa matarsa cutar, amma daga bisani sai ya yi kememe ya rika zargin ita ta sanya masa. A maimakon ya rufa mata asiri su nemi magani tare sai ya tayar da jijiyar wuya ya dora mata laifi don ya ci mutuncinta. Daga bisani idan iyayenta suka nemi su je a yi gwajin jini sai ya ki yarda, saboda ya san ba shi da gaskiya, ta haka sai auren ya lalace. Su kuma matan aure da ’yan mata su daina boyewa mazajensu ko masoyansu cutar da suke dauke da ita. Da zarar ka ga wacce kake so kuma ta fito ta gaya maka cewa tana dauke da wata cuta sai ka rungumi kaddara ka nema mata magani. Idan ka yi haka ka taimaka mata kuma za ka samu lada.
Saboda haka ya kamata maza su sauya tunaninsu kan irin wadannan cututtuka, su hada kai da matansu, ta yadda za su yaki kowace cuta don a gudu tare a tsira tare cikin rufin asiri.
Abubakar ya rubuto daga Legas: 08027406827