✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Mata 7 sun kone kurmus a hatsarin mota a Abekuta

Akalla mata bakwai ne suka kone kurmus sakamakon hadarin mota da ya auku a babbar hanyar Sagamu zuwa Benin. Kakakin Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen…

Akalla mata bakwai ne suka kone kurmus sakamakon hadarin mota da ya auku a babbar hanyar Sagamu zuwa Benin.

Kakakin Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa (TRACE) Babatunde Akinbiyi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.

Akinbiyi ya ce baya ga matan da suka kone, akwai karin wasu mutane bakwai da suka samu munanan raunuka.

A cewarsa hadarin ya auku ne da misalin karfe 2:50 na dare, kuma injin motar ne ya kama da wuta sakamakon fashewa da yayi.

“Motar ta taso ne daga Legas zuwa wani Coci a Epe albarkacin kusantowar Sabuwar Shekara, kwatsam sai injin dinta ya kama wuta.

“Mutane 15 ne a motar, kuma mata bakwai daga ciki sun kone, wasu bakwai kuma sun samu raunuka,” in ji shi.

Ya kuma ce wadanda suka samu raunin na kwance a asibiti suna jinya.