Akalla mata bakwai ne suka kone kurmus sakamakon hadarin mota da ya auku a babbar hanyar Sagamu zuwa Benin.
Kakakin Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa (TRACE) Babatunde Akinbiyi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.
- ’Yan sanda sun kashe ’yan bindiga 21, sun ceto mutum 206 a Kaduna
- WhatsApp zai daina aiki a wayoyin iPhone da Samsung Galaxy
Akinbiyi ya ce baya ga matan da suka kone, akwai karin wasu mutane bakwai da suka samu munanan raunuka.
A cewarsa hadarin ya auku ne da misalin karfe 2:50 na dare, kuma injin motar ne ya kama da wuta sakamakon fashewa da yayi.
“Motar ta taso ne daga Legas zuwa wani Coci a Epe albarkacin kusantowar Sabuwar Shekara, kwatsam sai injin dinta ya kama wuta.
“Mutane 15 ne a motar, kuma mata bakwai daga ciki sun kone, wasu bakwai kuma sun samu raunuka,” in ji shi.
Ya kuma ce wadanda suka samu raunin na kwance a asibiti suna jinya.