✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata 30 masu ilimi zamani sun shiga majalisar Shoura a Saudiyya

Gwamnatin Masarautar Saudiyya ta yi wa majalisar tuntubar kan harkokin mulki da zamantakewa ta ‘shoura’ gyaran fuska, inda ta nada mata masu zurfin ilimin zamani…

Gwamnatin Masarautar Saudiyya ta yi wa majalisar tuntubar kan harkokin mulki da zamantakewa ta ‘shoura’ gyaran fuska, inda ta nada mata masu zurfin ilimin zamani guda 30, a matsayin ’yan majalisar. Kuma daga cikin wadannan mata 30, mafi yawansu suna da digiri na uku, inda suka gudanar da ayyuka a jami’o’in kasar da kungiyoyin fafutikar hakkokin al’umma.

Sai wata marubuciya, ’yar jarida Kawthar Al-Arbash, wadda ta samu shiga wannan majalisa. Wannan mata ta kasance uwa ga wani dan Saudiyya da ya rasa ransa wajen tunkarar dan ta’addar kundiyar Daesh, da ya kai hari wani masallaci da ke birnin Dammam a bara.
Jerin wadannan mata masu ilimin zamani da Sarkin Saudiyya ya nada majalisar shoura, sun hada da:
1. Dokta Ahlam Mohammed Al-Hakim, shugaba ce a sashen ilimi da ke Jami’ar Jazan
2. Dokta Asma Saleh Al-Zahrani, mai bincike ce da ta kware a Falsafa da harshen Larabci. Ta ce tana fatan kasancewa muryar daukacin ’yan Saudiyya.
3. Dokta Jawaher Dhafer Al-Anizi, wata kwararriya a fannin nazarin fannonin ilimi da ta fito daga Jami’ar Ummul-kura ta Makkah. Dokta Ikbal Zain al-Abedin Darandri, kwararriya a fannin kididdigar lissafi da bincike.
4. Dokta Amal Salama al-Shaman, tana da digiri na uku a fasahar koyar da fannonin ilimi, wanda ta samu daga Jami’ar George Washington ta Amurka, ta samu shiga wannan majalisa tun a watan Janairun 2013.
5. Dokta Hamda Makbool Al-Joufi, tana da digiri na uku da ta samu daga Jami’ar Gimbiya Noura da ke Riyadh. A cewarta: “Ina godiya ga Sarki Salman da ya nada ni a matsayin ’yar majalisa. Shigata wannan majalisa na nuni da irin amintar da Sarkin Saudiyya da kima da mutumtakar mata, da irin matsayinsu a cikin al’umma.”
6. Dokta Hanan AbdulRahman Al-Ahmadi, wata Farfesa a fannin gudanar da harkokin kula da lafiya a Saudiya.
7. Raedah Abdullah Abunayan, tana da digiri na biyu, wanda ta samu daga Jami’ar Saud da ke Riyadh
8. Dokta Hanan Abdulrahman Al-Ahmadi
Sauran matan sun hada da: Dokta Zainab Abu Taleb da Dokta Samia Abdullah Bakhari da Dokta Sultanah Abdulmusleh Al-Bidwi da Dokta Aalia Mohammed Al-Dahlawi da Dokta Fatimah Al-Shehri da Dokta Fardous Saud Al-Saleh da Dokta Fawzia Aba al-Khail da Dokta Latifah Ashaalan. Mafi yawan wadannan mata kwararru a fannonin ilimi da likitanci da ayyukan sadarwa da difulomasiya.