Masu Zabar Sarki na Masarautar Zazzau sun mika wa Gwamna Nasir El-Rufai sunayen mutum uku domin ya zabi sabon Sarkin Zazzau daga cikinsu.
Mutanen da majalisar ta mika sunayensu daga cikin mutum 11 da ta tantance su ne:
- Iyan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu, wanda ya samu maki 89,
- Yariman Zazzau, Alhaji Muhammed Munnir Jafaru, maki 87, da kuma
- Turakin Karamin Zazzau , Alhaji Aminu Shehu Idris, mai maki 53.
Daga cikin sunayen ake fatar Gwamna El-Rufai ya zabi sabon sarki, ko da yake yana da ikon mayar da sunayen idan har bai gamsu da wadanda aka gabatar masa ba.
- Yadda ake zaben sabon Sarkin Zazzau
- Sarautar Zazzau: Mutum 8 na hankoron darewa kan karaga
- Yadda aka yi addu’ar ukun Sarkin Zazzau
Mutanen da suka bayyana sha’awarsu ta hawa kujerar a matsayin Sarkin Zazzau na 19 sun fito ne daga gidajen sarauta hudu na masarautar.
A ranar Alhamis masu zabar sarkin suka rufe karbar masu takarar zama Sarkin Zazzau na 19 domin tantancewa da fitar da mutum uku da suke ganin sun fi cancanta.
Tun washegarin rasuwar Sarkin Zazzau na 18, Alhaji Shehu Idris, masu zabar sarkin masarautar suka fara aikin fitar da wanda zai gaje shi domin cike gurbin.
Sarki Shehu Idris ya rasu ne a ranar Lahadi 20 ga Satumba, 2020, a Babban Asibitin Rundunar Sojin Kasa da ke Kaduna, sakamakon rashin lafiya da ya yi fama da ita.
Ya bar duniyar duniya yana da shekara 84, bayan ya shafe shekara 45 a kujerar Sarkin Zauzzau da ya dare a kai tun a 1975.