Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ke jihar Kano, Sheikh Umar Sani Fagge, ya ce akwai azabar da ke jiran masu kirkirar karya da yadata a shafukan sada zumunta na intanet.
Shehun malamin, wanda kuma Farfesan Larabci ne a Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK), ya yi wannan gargadi ne a wata lakca da ya gabata kan kafar sadarwa ta intanet, da dandalin sada zumunta da muhawara, da kuma yadda matasa ke amfani da su a yanzu.
- Amurka ce babbar kanwa uwar gami a rikicin Rasha da Ukraine — China
- An kama mai shekara 70 kan luwadi da yaro mai shekara 12
Ya bayyana irin narko da azabar da aka tanadar wa mai dabi’ar a lahira matukar ya mutu bai tuba ba.
“Za kwantar da mutum a rika yi masa zane a fuskarsa da faratan wuta, tun daga bakin gashinsa har zuwa karshen kuncinsa.
“Ana gamawa sai a juya daya kan kuncin nasa a sake nutsa wadannan farata na wuta, a zane ta kamar yadda aka yi waccan. Kafin a gama waccan da aka yi ya warke, sai a juya fuskar a maimaita,” inji malamin.
Ya ce haka za a yi ta yi wa mutum a wutar jahannama babu ranar da za a daina.
Daga karshe ya yi kira ga matasa da su san irin labaran da za su rika yadawa a intanet don guje wa fadawa cikin fushi da kuma azabar Allah idan sun mutu.
Wannan gargadi ya zo ne a daidai lokacin da ake kirkirar labaran karya a yada a intanet don jan hankalin masu amfani da shafukan na sada zumunta.