Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu, ya ce sukar lafiyarsa da wasu ke yi shirme ne tsagwaronsa.
Da yake zantawa da Tashar Freedom Radio ta Kano a Saudiyya, Tinubu ya ce ya yi Dawafi inda ya kewaye Ka’abah sau bakwai ya kuma yi Safa da Marwa wanda mara lafiya ba zai iya aikata hakan ba.
- Karatun jami’a na neman zama kwalele ga ’ya’yan talakawa
- ACF ta yi alhinin mutuwar Sarkin Ohanaeze Ndigbo
Masu sukar Tinubu sun dage da kira kan cewa dan takarar ba zai iya rike Najeriya ba saboda rashin koshin lafiya.
Sai dai Yinubun ya ce masu korafi game da lafiyarsa shirme ne kawai, saboda “Yanzu na kammala aikin Umarah, na yi Dawafi sau bakwai da Safa da Marwa da kaina.
“Shin wanda ba shi da lafiya zai iya aikata hakan? Don haka wannan tsohon labari ne, masu yayata hakan ba su da abin yi face karya da shirme.
“Kwarai ga ni a Saudiyya, bukatar kaina ta kawo ni. Tun fil azal ni mai sha’awar yin Umarah ne saboda dama ce ta ganawa da Ubamgiji,” in ji Tinubu.
Game da batun halartar tarurrukar tattaunawa da jama’a, Tinubu ya ce masu korafin ba a ganin shi a wajen tarurrukan wadanda suka sha kaye ne kuma haka za su ci gaba da shan kaye.
Ya ce a saninsa yana zagayawa don tattaunawa da jama’a walau kai tsaye ko kuma bisa wakilci.