✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu siyar da jaridu a Kano sun taya Kabiru murnar zama Shugaban kungiyar NPAN 

Hadaddiyar Kungiyar Masu Siyarwa da Rarraba Jaridu da Mujallu ta Jihar Kano, KUNMDA, ta taya Shugaban kamfanin Media Trust, mai buga jaridar Aminiya da Daily…

Hadaddiyar Kungiyar Masu Siyarwa da Rarraba Jaridu da Mujallu ta Jihar Kano, KUNMDA, ta taya Shugaban kamfanin Media Trust, mai buga jaridar Aminiya da Daily Trust, Malam Kabir Yusuf, murnar zama zababben Shugaban Kungiyar Masu Gidajen Jaridu na Najeriya (NPAN).

A ranar Talata 8, ga watan Nuwambar, 2020, Malam Kabir Yusuf, ya zama sabon NPAN, bayan an gudanar da zabe a sakatariyar kungiyar da ke Maryland a birnin Legas.

Kungiyar ta KUNMDA ta aike da wata wasika ta taya murna me dauke da sa hannun shugabanta, Sani Abdullahi da sakataren kungiyar, Abdullahi Umar tana bayyana cancantar Malam Kabir na jagorantar kungiyar.

“Wannan kungiya na taya ka murnar nasarar zama Shugaban NPAN. Mu Masu Siyarwa da Rarraba Jaridu da Mujallu a Jihar Kano, muna da yakinin za mu fi kowa amfana da sabon ofishin naka”, kamar yadda wasikar ta bayyana.

Sun kuma yi addu’ar fatan Allah Ya taya riko, Ya yi masa jagora kan sabuwar kujerar tasa, ya kuma kammala wa’adinsa lafiya.

“Allah Ya taimaki kungiyar NPAN, Allah Ya taimaki Daily Trust, Allah Ya taimaki KUNMDA. Mun gode”.