Gwamnatin Jihar Kano ta karrama wasu masu aikin sharan titi su bakwai a matsayin ma’aikatan da suka fi hazaka a watan Agusta, 2022.
Da yake mika takardar shaidar yabo, Shaddodi da kuma tsabar kudi ga masu sharar titin da aka karrama, Kwamishinan Muhalli na Jihar Kano, Dokta Kabiru Ibrahim Getso, ya ce an yi hakan ne don nuna godiya da kuma karrama ma’aikatan da suke aiki tukuru a fadin jihar.
- DAGA LARABA: Yadda ‘Sakacin Ma’aikata’ Ke Lakume Rayuka A Asibitin Murtala
- Kotu ta tsare magidanci saboda garkuwa da tsohuwar matarsa
Ya ce, “Wannan bidi’a ce da ma’aikatar ta bullo da ita da nufin inganta ayyukan ma’aikata a bakin aiki ba tare da la’akari da matsayi ko mukaminsu ba don wasu su zabe damtse wajen yin abin da ya kamata.”
Kwamishinan ya ci gaba da cewa ma’aikatar za ta ci gaba da zakulo irin wadannan ma’aikata da kuma karrama su a kowane wata.
Ma’aikatan da aka karrama sun hada da, Malam Ahmed Haruna, Sani Adamu, Kabiru Idris, Yusuf Usman (Sarkin Ruwa), Rabiu Abubakar da Alhaji Umar Nuhu (Baban Bola).
Da yake mayar da martani a madadin wadanda aka karrama Alhaj Umar Nuhu Baban Bola, ya bayyana jin dadinsu tare da yin alkawarin ci gaba da bayar da gudummawarsu wajen ganin an samu tsafta da lafiya a jihar.