✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu sayar da jarirai sun shiga hannu a Binuwai

Masu safarar mutane na yaudarar mata masu cikin shege su sayar musu da jarirai.

Wasu mutane da ke safarar jarirai sun shiga hannun hukuma a Jihar Binuwai.

Hukumar Hana Fataucin Mutane ta Kasa (NAPTIP), reshen Jihar Binuwe, ce ta sanar da cafke masu sayar da jiraran su biyu, wadanda ta ce za a gurfanar a gaban kotu da zarar kotuna sun dawo daga hutu.

Kwamandar NAPTIP, Shiyyar Jihar, Gloria Bai, ta sanar da hakan ne a hirarta da manema labarai kan nasarorin da hukumar ta samu a karkashin kulawarta.

Ta kara da cewa a cikin ’yan kwanakin nan, sau bakwai hukumar na samun kararraki kan fataucin da ya shafi kananan yara 13, wadanda aka yi nasarar ceto uku daga cikinsu.

“Akwai samari biyu da aka dauko daga Gboko aka sayar da su a Jihar Legas; An cafke wadanda suka sayar da su kuma suna gaban kotu; An ceto yaran ne da taimakon ’yan sandan,” inji ta.

Yadda ake yaudarar masu cikin shege

Kwamandar shiyyar ta kuma bayyana damuwa kan yadda ’yan mata ke haihuwa ba tare da aure ba, wasu daga cikinsu ma ba su san wanda ke da alhakin yi musu cikin ba.

Ta kara da cewa, “Masu fataucin sun fara amfani da wannan damar, suna cin karensu babu babbaka ta hanyar amfani da irin wadannan ’yan mata saboda rauninsu, wasunsu ma korar su daga gida ake yi bayan daukar ciki.

“Masu fataucin suna amfani da wannan damar wajen yaudarar irin wadannan ’yan mata, su kai su wani wuri, su sayar musu da jariran, mun samu bayanai da dama a kan hakan.

“A yanzu haka mun cafke mutum biyu da ake zargi mambobin kungiyar da ke yaudarar ’yan mata masu juna biyu da suka haifi jariran kuma bayan haka sun sayar da jariran.

“Mun samu labarin akwai lokuta da aka gaya wa wasu daga cikinsu cewa jariran sun mutu kuma ba a ba su kobo ba wasu kuma an biya su abun da bai taka kara ya karya ba.”

Bai ta bayyana yadda aka kai wata yarinya Jihar Abiya aka sayar da jaririnta sannan aka ba ta N100,000, da kuma shari’ar wata mata daga Jihar Bayelsa da ta sayi jariri a Binuwai, kuma har yanzu ba a dawo da jariran ba.