✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu riga da ƙaro na mana shisshigi a aikin tsaro a Gombe — Cibil Difens

Na lura mutanen Gombe ba su yarda da a kama mai laifi ba.

Kwamandan Hukumar Tsaro ta Cibil Difens a Jihar Gombe, Muhammad Bello Mu’azu, ya koka kan yadda masu riga da ƙaro ke musu shisshigi wajen tsoma baki da zarar sun kama mai laifi.

Muhammad Bello Mu’azu, ya ce jama’a su sani shi ba a yi masa haka, muddin wanda aka kama mai laifi ne to su je kotu su karbe shi ba a wajensa ba, domin duk girman mutum muddin ya aikata laifi zai kama shi kuma ba maganar beli.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa da ke Gombe.

Kwamandan ya bayyana cewa tun farkon zuwansa Gombe ya zaga wasu unguwanni da suke da tarihin rashin tsaro, inda ya gane wa idonsa yadda ake aikata ta’asa amma babu wani da ya zo ya kawo shawarar yadda za a samu mafita.

Ya ce sai bayan da ya fara gudanar da aiki sannan mutanen wasu unguwanni suka je ofishinsa suna kukan halin da suke ciki.

Ya ce ya bayyana wa musu koken cewa mafita daya ita ce su samar da wajen da jami’an sa za su yi aiki a matsayin Ofis sai ya tura musu jami’an a bude karamin ofishi amma har kawo yanzu babu wata unguwa da ta ce ga waje ta shirya.

“Na lura mutanen Gombe ba su yarda da a kama mai laifi ba, hakan ne ya sa suke daure wa mai laifi gindi domin duk tsananin laifin mutum sai kaga wani ya sanya babbar riga ta sha ƙaro ya zo ya ce yana son a saki wanen nan da ake tsare da shi saboda wata bukatarsa ko ta wasu manya da suka turo shi”

Kwamandan ya kira yi al’umma da cewa idan suna son aiki ya tafi daidai sai sun daina yi musu shisshigi sun ba su haɗin kai domin yin shisshigi a aikin hukuma musamman a harkar tsaro yana kawo musu cikas.

Ya kuma bai wa irin wadannan masu riga da ƙaron cewa su kiyaye don muddin aka samu mutum da laifi, sannan wani ya biyo baya don neman a sake shi ba tare da ya yi la’akari da laifin da ya yi ba, to ya sani zai hada da shi ya rufe saboda hakan ya zama darasi ga wasu.

Kazalika, ya ce ba cibil difens kadai ake yi wa wannan shisshiga ba dukkan jami’an tsaro ne don haka su daina, yana mai cewa haɗin kai suke bukata daga gare su.