Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya soki masu ra’ayin rikau na kasar, inda ya ce matasan da suka shafe kwana goma suna zanga-zanga a titunan kasar, suna bukatar fiye da abin da masu ra’ayin rikau za su iya bayarwa.
Shugaba Rouhani ya fadi a ranar Litinin da ta gabata cewa, “Zai kasance muguwar fassara (ga zanga-zangar) kuma cin fuskar mutanen Iran a ce (masu zanga-zangar) suna yi ne kawai a kan matsin tattalin arziki.”
Kamfanin Dillancin Labarai na Tasnim ya ruwaito Shugaba Rouhani na cewa: “Babu wanda zai tilasta salon rayuwarsa ga matasa masu tasowa… matsalar ita ce muna son samar da al’umma iri biyu a bayanmu kuma su rayu a irin hanyar da muke so.” Ya ce masu zanga-zangar suna da bukatu na siyasa da harkokin rayuwa.
Ana ganin jawabin na Shugaba Rouhani mara wa matasa da kananan ma’aikatan da suke zanga-zangar a biranen kasar baya ne.
Zanga-zangar wadda ta faro daga tsadar kwan kaji ta rikide zuwa ta tawaye ga shugaban addini na kasar, Ayatollah Ali Khamenei wanda masu zanga-zangar suka rika fadin munanan kalamai a kansa.
’Yan siyasa a Iran sun yi ta dora wa abokan hamayya laifin aukuwar zanga-zangar, inda wadansu magoya bayan Shugaba Rouhani suka ce masu ra’ayin rikau ne suka shirya zanga-zangar don tozarta gwamnati, sun ce, masu ra’ayin rikau din sun shirya zanga-zangar ce domin su nuna tsare-tsaren tattalin arziki na Shugaba Rouhani sun gaza. Kamar yadda wani mai nazari da sharhi dan kasar Iran, Adnan Tabatabai ya shaida wa kafar labarai ta Newsweek. “Ta hanyar kalamansa, sai ya karkatar da fushin mutane zuwa kan wadansu shugabannin,” inji shi.
Sai dai wadansu na ganin babu alfanun kalaman Shugaban matukar bai dauki matakai masu karfi da suka hada da sako daruruwan masu zanga-zanga da aka tsare tun fara zanga-zangar ba.
“Duk da cewa Rouhani ya tabo ainihin abubuwan da mutane suke da tambayoyi a kai, amma samar da dama daidai-wa-daida ga kowa kuma kowa ya biya haraji… ya gaza kawo cikakkiyar mafita,” Omid Memarian, wani manazarci dan Iran ya shaida wa Newsweek. “Maimakon haka, sai ya soki daya bangaren ba tare da ambatar suna ba. Irin dai tsohon labarin da aka saba ji. Mutane kuma aiki suke son gani,” inji shi.