Sarkin Maru Jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Maigari, ya dora laifin ci gaban ayyukan ’yan bindiga a Jihar a kan masu yi wa ’yan bindigar leken asiri.
Sarkin Maru ya bayyana hakan ne yayin da yake kira ga sabon Kwamishin ’Yan Sandan Jihar, Abutu Yaro, wanda ya ziyarce shi, da ya mayar da hankali sosai kan masu kai wa ’yan bindiga bayanai domin kawo karshen ayyukan maharan.
- Hamar: Kabilar da mata ke shan duka kafin a aure su
- ‘Dalilin da muka hada bikin shan rake’
- Lambar NIN: Ba za a rufe layukan waya ba
- Sai mun ga bayan ta’addanci a Najeriya a 2021 —Buhari
“Muna rokon gwamnati da hukumomin tsaro da su dauki kwararan matakan magance masu kai wa ’yan bindiga bayanai.
“Yawancin masu yi musu leken asiri na al’umma, mutane sun san su; suna harkokinsu cikin jama’a ba tare da jin shakku ko an yi maganin su ba.
“Muna kira ga hukumomin tsaro su mayar da hankali a kansu, su kuma yi maganin su,’’ inji Sarkin Maru.
Tun da farko, CP Yaro ya ce ya ziyarci sarkin ne domin samun hadin kan muhimman masu ruwa da tsaki, musamman sarakuna, domin samar da aminci a Jihar Zamfara.
Kantoman Kabar Hukumar Maru, Alhaji Salisu Dangulbi, wanda ya halarci ganawar ya yi kira da a tura karin jami’an ’yan sanda zuwa yankunan Karamar Hukumar da suka fi fama da matsalar tsaro.
“Don Allah, yankuna irinsu Mayanchi da makwabtansu na neman taimakon gaggawa; muna bukatar karin jami’an tsaro a yankin cikin gaggawa domin a samu nutsuwa,’’ inji Dangulbi.
Ya ba wa Kwamishinan ’Yan Sandan tabbacin samun karin goyon baya da karamar hukummar domin magance matsalar da ta adddabi jihar.
CP Yaro ya kuma yi makamanciyar ganawar da shugabannin addini da sauran sarakuna da masu ruwa da tsaki a karamar hukumar da zummar shawo kan matsalar tsaron.