✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu kwacen waya sun hade da ‘’yan Yahoo’ a Kano

Suna sayar wa masu kutsen intanet layukan wayan su saci kudi daga banki.

Masu kwacen waya da masu kutse ta intanet a Kano sun hada kai ta yadda suke ci gaba da cutar da mutane a birnin Kano da kewaye.

Aminiya ta gano cewa masu kwacen wayar na sayar da layukan wayoyin da suka kwace ga masu kutse ta intanet, wadanda ke amfani da layukan su samun bayanan bankin mai wayar, su ciri kudi daga asusun bankinsa.

Mazauna garin Kano da dama da suka yi gamo da masu kwacen waya sun bayyana irin tashin hankalin da suka gani gomon nasu, wanda yawanci ke raba su da dukiyoyinsu ko illata su, idan ma sun sha ke nan.

Tsananin lamarin ya kai ga matasan da ke kwacen wayan suna yin zuga su tare ababen hawa da tsakar rana suna kwace wa mutane wayoyi ko wasu kadarorinsu.

A wasu lokutan, idan mutum ya ja da su, ko ya bi su zai kamo su, ko suka ji tsoron shi, sai su yi masa rauni da makami ko ma su kashe shi.

Hakan na faruwa ne duk da kokarin da hukumomin jihar ke yi na kawar da ayyukan laifi da ’yan daba, wadanda a wata shidan farkon shekarar 2021 aka tsare daruruwansu.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ce an samu saukin matsalar kwacen waya bayan wasu matakai da ta dauka domin kawar da bata-garin.

Amma mazauna garin Kano na cewa har yanzu ’yan dabar da hadin bakin masu kutse ta intanet na ci gaba da cin karensu babu babbaka, wanda ya ma fi karfin raba su da wayoyinsu.

Ana samun layinka, shi ke nan

Aminiya ta gano cewa masu kutse ta intanet din na amfani da layukan wayan da masu kwacen waya suka sayar musu su samu lambar BVN din bankin mai layin wayar, ta hanyar tura sakon USSD.

Idan aka turo lambar BVN din da aka hada layin da shi, sai su rika amfani da BVN din suna yin huldar banki da layin, su yi ta zarar kudi daga bankin mai wayar ko sayen kati ko wasu sayayya na makudan kudade.

Aminiya ta gano cewa, saboda hakan wasu masu kwacen da ake gani “masu kirki ne”, kan yi wa mai wayar da suka kwace tayin layin SIM dinsa, ya saya sannan su tafi da wayar.

Sun kwashe mana kudade

Hajiya Umma Hassan da ke unguwar Sabuwar Gandu ta ce bayan an sace mata waya da ’yan awanni aka yi ta amfani da layin wayar ana cirar kudi daga bakinta.

Ita ma Amina Salisu da ke zaune a unguwar Tudun Murtala da ke birnin Kano ta bayyana mana abin da ya faru da ita.

“Sun sace mana wayoyi hudu tare da kwamfutar dana kuma da ma mijina ba ya nan, ya yi tafiya.

“Kafin ranar da dare ya turo mana N192,000 na cefane da biyan kudin makarantar yara a asusun bankin dana.

“Washegari da safe dan nawa ya je zai ciri kudin a banki, ya samu an kwashe gaba daya.

“Da ya bincika, sai bankin suka tabbatar masa cewa an ciri kudin ne da misalin karfe shida na safe.”

Wani jami’in kanfanin sadarwa na Fantel Telecommunication da ke garin Kano ya shaida wa wakilinmu cewa wani mutum ya kawo musu korafi cewa an sace wayarsa, da ya kai korafi banki, sai suka shaida masa cewa an sayi katin waya na  N140,000 da layin wayar tasa da aka sace.

Kare SIM daga masu kwacen waya

Wani jami’in kamfanin Fentel, Sharif Abbas, wanda ya tabbatar da samun irin wadannan korafe-korafe daga kwastomominsu ya yi kira ga mutane da su kasance masu lura sosai, sannan hukumomin tsaro su fuskanci matsalar masu kutse ta intanet gadangadan.

A cewarsa, kamfanonin sadarwa sun riga sun samar da hanyoyi masu sauki da masu waya za su kare layukan SIM dinsu daga fadawa tarkon bata-gari.

Daga ciki akwai amfani da lambar sirri ta PIN din da kowane SIM  yake da shi su kulle layukansu kamar yadda mutum ke kulle wayarsa da lambobin sirri.

Ya ce abu na farko shi ne mutum ya tabbata ya sauya lambar PIN din layin SIM dinsa, domin kowane sabon SIM yana zuwa da 0000 a matsayin lambar PIN dinsa na farko.

To ana so mai layin wayar ya canza lambar wadda yake so, wadda zai iya tunawa da sauri, saboda ko da wayar ta fada a hannun bata-gari, ba za su iya bude layin ba, ballanta su samu wani bayani daga cikin layin.

Abbas ya kuma shawarci bankuna da su dauki mataki a kan matsalar ta hanyar neman lambar PIN din asusun ajiyar a duk lokacin da za a yi amfani da tsarinsu na USSD; lambar PIN din ta zama ita ce abin da za su yi amfani su tabbatar da sahihancin cinikin sannan su amince.

Kakakin ’yan sanda Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, da muka tuntuba ya ce Rundunar tana aiki ka’in da na’in domin yakar ayyukan kwacen waya da sauran laifuka a jihar.

Ya ce a baya-bayan nan Rundunar ta tsare ’yan daba akalla 95 masu kwacen waya, aka kuma gano wayoyi 34 da wasu kayayyaki a hannunsu.

Al’amarin kwacen waya da satar kudade daga banki ta hanyar amfani da layukan wayoyin da aka sace ko aka kwace ya zama ruwan dare a sassan Najeriya.

Mutane da dama da hakan ta faru da su sun ce sun rasa kudade masu dimbin yawa, wani lokaci kafin su je banki su sanar, miyagun sun riga an kwashe kudade