Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabimila, ya kalubalanci masu shakku a kan ainihin shekarun dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, da su je su tambayi mahaifiyarsa da ta rasu shekaru tara da suka wuce.
Kakakin ya fadi hakan ne a cikin bakar magana ga masu tuhumar ainihin shekarun haihuwar dan takarar na APC a zaben 2023 mai zuwa.
- NAJERIYA A YAU: Me Ke Sa Tinubu Baya-baya Da Shiga Jama’a?
- Dan Majalisar da ya yanke jiki a taron yakin neman zaben Tinubu ya rasu
Gbajabiamila ya fadi hakan ne a wani taron gangamin yakin neman zaben Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima da aka gudanar a Legas a ranar Asabar.
“Ainihin shekarun haihuwar Tinubu su ne wadanda mahaifiyarsa ta ambata da cewa su ne shekarunsa, duk wanda ya ke shakka sai ya je ya same ta, ta tabbatar masa da hakan ne ko a’a,” inji Gbajabiamila.
An dade ana ce-ce-ku-ce kan ainihin shekarun haihuwar Tinubu, yayin da ya yi ikirarin shekararsa 70 da haihuwa, ’yan adawa da sauran ’yan gaza-gani na cewa, ya wuce haka.
Ya kuma fadawa taron magoya bayan dan takarar cewa, wanda duk ya tambaye su matakin ilimin Tinubu, su ce shi ne wanda ya fi duk ’yan takarar ilimi, idan an kuma tambaye su Amurka na nemansa, su ce ta fi kowa bincikensa, amma ba ta same shi da wani laifi ba.
Alhaja Habibat Mogaji, mahaifiyar Tinubu ta dade da rasuwa, tun cikin watan Yunin shekarar 2013.