✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu karbar haraji na takura mana – Fatake

Masu fataucin dabbobi da kayan abinci daga yankin Arewacin kasar nan zuwa Kudanci sun koka bisa yadda ake takura musu bisa biyan haraji musamman tsakanin…

Masu fataucin dabbobi da kayan abinci daga yankin Arewacin kasar nan zuwa Kudanci sun koka bisa yadda ake takura musu bisa biyan haraji musamman tsakanin hanyar Kano zuwa Zariya.
Har ila yau, sun yi kira ga  gwamnatin Jihar Kano  da ta shiga tsakanin ‘ya’yan kungiyar da wasu da suke ikirarin cewa su jami’an karbar haraji ne kan wannan hanya.
Shugaban kungiyar Masu Fataucin Dabbobi da Kayan Abinci na kasa, Alhaji Mohammad Tahir shi ne ya yi wannan kiran bayan kammala wani taron gaggawa da kungiyar ta kira kwanakin baya dangane da yadda al’amarin karbar haraji “ke neman wuce gona da iri.”
Shugaban ya ce kungiyarsu tana bin duk wani sharadin gwamnati, kuma ba ta wasa wajen biyan haraji saboda muhimmancin sana’arsu, amma ya ce, “ba za mu yarda a rika takura mana ba da sunan karbar haraji wanda ba ya cikin hurumin doka.”
A karshe ya bukaci Gwamnatin Jihar Kano da ta sa baki tsakaninsu da wadannan mutane.
“Ta kuma tsara yadda ya kamata a rika karbar harajin wato a wajen daukar kaya da wajen saukewa, wanda hakan  ka’ida,” inji shi.