✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Masu jiran hukunci sun fi wadanda aka yanke wa yawa a gidajen yarin Najeriya’

Ya yi kira ga alkalai da su gaggauta yanke hukunci a kotunansu.

Sanata mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu a Majalisar Dattijai, Ali Ndume ya ce wadanda ke jira a yanke masu hukunci a gidan yari sun fi wadanda aka yanke wa yawa a Najeriya.

Sanatan na wadannan kalaman ne yayin hirarsa da Aminiya kan halin da ya tsinci gidan yari lokacin da aka kulle shi a Kuje, a Abuja.

A cewarsa, yawan mutanen da suke cikin jira a yanke masu hukunci sun wuce yadda a ke tunani, lamarin da ya ce shi ke kara cunkoso a gidajen yarin kasara nan.

Ya kara da cewa duk da yake gidan yari ba wurin hutu bane, yana da kyau a samar da wadataccen muhalli ga wadanda ke tsare, kuma su sami kyakkyawar kulawa.

Daga karshe yace ya kamata alkalai su rika kokari wajen gaggauta yanke hukunci, saboda kin yin hakan kamar tauye hakkin hakkin daurarrun ne.